Zanga-Zangar Juyin Mulkin: An Kashe Mutane 10 a Sudan

 

An kashe akalla mutum 10 tare da jikkata gwammai a Khartoum, babban birnin Sudan, bayan da sojoji suka bude wa masu zanga- zanga wuta.

Rahotanni sun ce an jibge tarin jami’an tsaro a birnin an kuma rufe gadojin da ke isa cikin Khartoum.

‘Yan kasar ta Sudan na bore ne a rana ta biyu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi ranar Litinin.

Kawo yanzu babu masaniyar inda Firaiminista Abdalla Hamdouk da wasu ‘yan siyasa suke.

Tuni kasashen duniya suka yi alla-wadai da matakin sojojin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here