‘Yan Bindiga Sun Kashe Masallata 18 a Jahar Neja

 

Rahotanni daga jahar Neja da ke tsakiyar Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum 18 a kauyen Maza-Kuka da ke karamar hukumar Mashegu ranar Litinin.

Wani da ya tsira a harin ya fada wa kamfanin dillacin labaran Reuters cewa maharan sun isa kauyen ne a kan babura ana tsakiyar sallar Asuba suka bude wuta a cikin masallaci.

Ya kuma ce yan bindigar sun jikkata mutum 20, suka kuma tafi da sama da mutum 10.

Hare-hare da satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da ta’azzara a arewacin Najeriya, inda aka kashe daruruwa a bana, musamman a arewa maso yammaci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here