Zanga-Zanga: An kashe Mutane 5 a Lebanon
An harbe mutane biyar har lahira a Beirut babban birnin Lebanon a lokacin wata zanga zanga ta nuna adawa da binciken da ake gudanarwa game da nakiyoyin da suka fashe bara a tashar jiragen ruwa.
Magoya bayan kungiyar Hizbullah ta yan shiah, da wasu masu mara masu baya ne suka yi cincirindo suna neman a cire alkalin dake shugabantar kwamitin binciken.
Magoya bayan kungiyoyin Hezbollah da Amal sun taru a kusa da ma’aikatr shari’a suna nuna bacin ransu kuma suna cewa lallai sai an sauke alkali Tarek Bitar.
Akwai damuwa sosai kan binciken da ake yi kan fashewar da ta auku a tashar jirgin ruwan birnin, har ta kai Hezbollah na tuhumar alkalin da nuna rashin adalci ga wasu tsofaffin ministocin gwamnatin kasar da su ke da alaka da ita.
Rundunar sojojin Lebanon sun tura dakarunta masu yawa domin shawo kan lamarin kuma ana iya jin karar harbin manyan bindigogi a titunan birnin.
Masu zanga-zanga sun ce an rika harbinsu daga saman wasu gidaje.
Tun da farko, wata kotu ta yi watsi da wata karar da biyu cikin ‘yan siyasar kasar da alkali Bitar ya bukaci su bayyana a gabansa domin tuhumar da ake yi musu ta rashin iya aiki.
Iyalan wadanda fashewar da ta auku a tashar jirgin ruwan ta rutsa da su sun yi tir da wannan matakin na alkalin, wanda ya tilasta aka dage binciken a karo na biyu cikin mako uku.
Suna kuma zargi cewa shugabanni na siyasa a kasar na kokarin kare kansu da manyan jami’an gwamnati daga wannan binciken.
Babu wanda aka samu da laifi tun bayan aukuwar fashewar a watan Agustan 2020, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 219 baya ga mutum 7,000 da su ka sami raunuka da kuma dubban gidaje da gine-gine da su ka ruguje.