Kotu ta Saka Ranar Zartar da Hukunci Kan Dakatar da Kafar Sada Zumunta ta Twitter
Kotun kasashen yammacin Afrika da ke Abuja na shirin yanke hukunci kan dakatar da kafar sada zumunta ta Twitter da hukumonin Najeriya suka yi.
Kotun ta saka ranar 22 ga watan Janairun 2022 a matsayin ranar da za ta zartar da hukunci, kan karar da kungiyar masu fafutika ta SERAP ta shigar, inda ta ke kalubalantar gwamnatin Najeriya na rufe shafin.
A cewar SERAP matakin hukumomin tauye hakkin ‘yan Najeriya ne da ya shafi ‘yancin fadar albarkacin baki.
Read Also:
A zaman farko-farko da ta yi ranar 22 ga watan Yunin 2021, kotun ta umurci gwamnatin Najeriya da ta janye batun hukunta gidajen jaridu da sauran kungiyoyi dama dai-daikun jam’a da suka yi amfani da Twitter yayin da ake kan sauraren karar.
A farkon watan Yuni ne gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dakatar da Twitter daga aiki a Najeriya, bayan da kamfanin ya sauke wasu kalaman Shugaban, da ya ce sun saba wa dokokin amfani da Twitter.
Sai dai tun bayan rufe shafin, ‘yan Najeriya da dama sun koma amfani da manhajar Virtual Private Network (VPN) wurin bude shafukan nasu.