Zazzabin Cizon Sauro na Ci gaba da Addabar Al’ummar Jihar Kano
Yayin da yanayi ya fara sauya wa zuwa sanyi, a jihar Kanon Najeriya har yanzu sauro na ci gaba da addabar al’umma.
Daruruwan mutane ne ke tururuwa zuwa asibitoci don neman maganin zazzabin cizon sauro, inda suke bin dogon layin ganin likita.
Wakilin BBC Hausa Zahraddeen Lawan ya je asibitin kwararru na Murtala Muhammad don ganin yadda suke fama.
Ya ce bayanan da ya samu na cewa fiye da rabin mutanen da ke jiran ganin likita a wajen zazzabin maleriya ne ya kai su.
Read Also:
Dr Safiya shugabar sashen kula da kananan yara a asibitin na Murtala ta ce ba su yi mamakin rashin raguwar zazzabin ba, saboda sauro har yanzu yana ci gaba da ƙyanƙyasa.
Marasa lafiya da dama ba sa iya sayen magani, amma Dr Safiya ta ce akwai abin da gwamnati take yi.
Da dama dai ba sa iya jure wa dogon layi a asibiti, yayin da wasu kuma ba su da kudin da za su iya magani, al’amarin da ya sa wasu ke zuwa shagunan sayar da magani.
Sai dai ko a can din ma ana ganin akwai tarin jama’a kamar asibiti.
A baya-bayan nan dai, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da gidauniyar kawo karshen zazzabin cizon sauro inda hukumomi suka ce ana bukatar kusan naira tiriliyan biyu, don rage yawan cutar da mace-macen da take haddasawa nan da shekara ta 2025.
Masana sun ce cutar tana ci gaba da addabar jama’a musamman kananan yara da mata masu juna biyu.