Gwamnatin Zimbabwe za ta yi wa Ma’aikatan ƙasar ƙarin Kashi 100 na Albashi
Gwamnatin ƙasar Zimbabwe za ta ƙara wa ma’aikatan ƙasar albashi da kaso 100, a wani ɓangare na inganta jin daɗin ma’aikatan, kamar yadda kafar yaɗa labaran gwamnatin kasar ta ruwaito.
A wata sanarwa da ma’aikatar kudi ta kasar ta fitar, ta ce sabon tsarin albashin ya ƙunshi ƙarin dala 250 na ƙuɗaɗen alawus-alawus ɗin corona ga duka ma’aikatan ƙasar, da kuma ƙarin dala 80 a kowane wata ga malaman makaranta.
Read Also:
Sanarwar ta ce ƙarin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Maris ga ma’aikatan fannin tsaro, sai kuma 1 ga watan Afirilu ga duka sauran ma’aikatan ƙasar.
Wakilan ƙungiyar malaman makarantar ƙasar sun ce ƙarin albashin ‘abin a yaba’ ne, to amma sun ce ƙarin alawus ɗin da aka yi na korona ya yi kaɗan.
Wakilan kungiyar ma’aikatan jinya sun ce an tsara gudanar da ganawa ranar Laraba kan alawsu din koronan.
A shekarar 2020, gwamnatin Zimbabwe ta ce ba za ta iya yin ƙarin albashi ba a daidai lokacin da likitocin ƙasar suka shafe fiye da wata hudu suna yajin-aiki, lamarin da ya ƙara kawo naƙasu ga fannin lafiyar ƙasar.