A yanzu dai muna gab da shiga shekarar zabe ta 2019. A wannan shekara ne al’ummar Najeriya kusan miliyan 70 zasu fita rumfunan zabe domin sake zaben sabbin Shugabannin a wani sabon zangon mulkin demokaradiyya da zamu shiga, wannan zabe shi je karo na 6 tun bayan da aka dawo mulkin demokaradiyya a Najeriya a shekarar 1999.
A saboda haka muke ganin a wannan lokacin ‘Yan Najeriya da zasu yi zabe sun san inda yake musu ciwo kuma zasu bambance tsakanin aya da tsakuwa a shugabanni da kuma wakilai a majalisun dokoki na tarayya da na jihohi.
Wannan zabe zakaran gwajin dafi ne wajen nuna balagar Najeriya a mulkin demokaradiyya. Domin kuwa yanzu ne lokacin da al’umma zasu bayyanar da sanin ciwon kansu kuma su nuna cewar sun san hakkinsu sun kuma san cewar su ‘ya ‘ya ne ba mallakar wasu tsiraru ba.
Lokaci yayi da al’umma zasu fito Kwai da kwarkwata su bayyanawa duniya cewar suna da ‘yanci kuma zasu kare wannan ‘yanci nasu. Ya hanyar fitowa subi layin zabe su kadawa mutanan da suke so kuri’unsu domin su shugabance su ko su wakilce su.
Dole ne a lokacin da ‘Yan Najeriya suka fita rumfunan zabe domin zaben sabbin Shugabanni da kuma wakilai su Sani cewar, su wakilai ne na al’ummar dake da rauni masu bukatar taimako na gaskiya, dole ne, masu zabe su sani cewar amana ce Allah ya danka a hannunsu wajen zabarwa ‘ya ‘yansu da jikokinsu shugabannin da zasu jibanci al’amarinsu kuma su dora wannan kasar tamu akan gwadabe mai kyau.
Zabe yana daga cikin amanar dake kan duk wani dan Najeriya. Kuma dole ne kowa ya sani kuma ya sakankance cewar Allah zai tambaye shi akan wannan amana. A saboda haka, a yanzu babu batun mutane su yi zabe domin a biyasu ko a sayi kuri’unsu. Tilas mutane suyi zabe na gaskiya bisa fahimtar irin kalubalen da ke gabansu musamman halin da kasar take ciki a yanzu na tabarbarewar tattalin arziki da tarbiyya da tsaro da kuma uwa uba, karuwar al’umma dabake samu cikin sauri a wannan kasa.
A wani taro da aka gabatar a Kano a wannan makon a jihar Kano kan Boko Haram da irin illolin da ya yiwa al’umma Najeriya. A wajen taron mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu yake bayyana cewar Daga nan zuwa shekaru ashirin masu zuwa, kididdiga ta nuna cewar za a samu ‘Yan Najeriya mutum miliyan dari wadan da Sallari matasa ne daga shekaru 18 zuwa 40, inda ya Kara da cewar idan har bamu tashi tsaye wajen dora kasarnan akan gwadabe na gaskiya ba, to za a wayi gari bala’in da yake tunkaro mu yafi na Boko Haram din yanzu.
Wannan magana ta Mai Martaba Sarkin Kano abin tsoro ce kwarai kuma abin a tsaya ayi mata duba na tsunaki ce, domin wadannan matasa miliyan dari suna bukatar abinci da tufafi da wajen kwana da kuma aikin yi, idan kuwa babu wani tanadi akan haka to akwai abin tsaro kwarai da gaske. Domin zinace zinace da sace sace zasu yi kamari.
Tun yanzu al’Umma sun san irin halin da ake ciki na yawan sace sace da barace barace, dukkan kasuwanni da masallatai da tashoshin mota da guraren taruka sun zama tarkon mabarata da barayi, yanzu kana ji kana gani za a murdeka a kwace maka waya ko kudi mutane suna kallo ba abinda zasu yi, Yara matasa suna abubuwa na fitsara ana bayyana tsiraici da alfasha a sarari babu kunya babu tsoron Allah.
Duk wadannan abubuwa suna faruwa ne saboda rashin nagartattu kuma ingantattun shugabanni. Al’umma ya zama bata san ciwon kanta ba, mutane sun mayar da kansu hajar sayarwa a kasuwa, mutum yaje ya nemo kudi na halal da na haram ya zo yana rabawa mutane domin su zabe shi, idan akai rashin sa’a aka hadu da wawayen mutane su karbi kudi su zabe su.
Dole ne iyaye da Malamai da Sarakuna su bayyanawa al’umma zahirin al’amari dangane da batun Shugabanci da kuma amfaninsa da muhimmanci na zaben mutanan kirki dan su jagoranci al’umma, wannan wajibi ne da kusan yake kan kowa, mutane suna kishirwar samun adalai kuma ingantattun shugabanni domin tsamo al’umma daga mawuyacin halin bala’in talauci da fatara da yunwa da kazanta da cututtuka.
Lallai ya zama wajibi al’umma a wannan lokacin su tashi tsaye su gayawa kansu gaskiya. A fito a zabi mutanan kirki masu amana masu gaskiya wadan da zasu hidimtawa al’umma. Ba mutanan da zasu sace dukiyar al’umma su azurta kansu da iyalansu da surikansu, sannan daga bisani su nunawa wawayen mutane cewar gasu a zabe su, wanda Wannan shi ne tabewa da koma bayan tunani idan mutane suka bi irin wadannan mutane, ba daidai bane, mutum ya kwashe kudin al’umma ya azurta iyalansa da surikansa sannan daga bisani yace a zabe su zasu yi gaskiya zasu yi aiki tukuru.
Wannan yaudara ce kuma karya ce tsagwaronta. Mutane su tashi su nunawa irin wadannan gurbatattun Shugabanni cewar su ba kayan gadonsu bane, su nuna musu cewar yanzu ba da bane, su gwada musu cewar zaben 2019 ya sha bamban da kowane zabe, Domin kuwa zabe ne wanda za a yi na Kai Da Halinka. Idan kai mutumin kirki ne al’umma sun sani, idan kuma yaudara ka zo da ita nan na al’umma sun sani kuma ba zasu Baka dama ba ka sake cutarsu.
Mutanan da aka yi musu shaida da gaskiya da adalci da rikon amana da tsare dukiyar al’umma sune irin mutanan da al’umma ya dace su sanya a gaba, sure amince musu su basu amanar dukiya da mutuncinsu. Idan suka yi haka suka zabi mutanan kirki shi ne suka yi abinda ya dace kuma shi ne suka taimaki al’ummar da zasu zo nan gaba.
Idan mutane suka dora komai a inda ya dace akwai tabbacin samun ingantacciyar rayuwa da walwala da tsare amana da rayuwa da kuma dukiyar al’umma. Lallai al’umma su tashi tsaye akan wannan zaben su fadakar da iyalansu da abikansu da dangi da ‘Yan uwansu wajen ganin an zabi mutanan kirki masu amana masu manufa wadan da al’umma ce a gabansu ba abinda zasu samu su da iyalansu ba.
Haka kuma, kada jama’a su bi rudin shaidanu wadan da zasu kawar da hankalinsu akan mutanan kirki a nuna Mas’udu cewar ga zance ga magana, lallai mutane su yi watsi da duk wasu da zasu zo suna kushe mutanan kirki dan basa jam’iyya daya da su.
Kada mutane su yi la’akari da jam’iyya, su fito su yi la’akari da mutanan kirki ko a wace jam’iyya suke, kada mutane su kalli jam’iyyar, su kalli mutanan, shin zasu Iya tsare musu mutunci da dukiya da amana indai zasu yi haka mutane su danka musu amana ko a cikin wacce jam’iyya suke yin takara.
The post 2019: Zabe ne na kai da halinka – Yasir Ramadan Gwale appeared first on Daily Nigerian Hausa.