2021: Za’a Fara Rajistar Tafiya Aikin Hajji
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta buɗe ƙasar rajistar aikin Hajjin 2021.
Hukumar ta bayyana sa ran ta cewa Saudiyya za ta iya ba da damar aikin Hajjin.
Hukumar ta umarci jihohi da su fara rajistar Hajjin da Umarah na 2021.
Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), a ranar Litinin, ta fada wa shugabannin hukumomin mahajjata na jihohi su ci gaba da rajista da shirye-shiryen aikin Hajji da Umrah na 2021.
Read Also:
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban ta na Hulda da Jama’a, Fatima Sanda, Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunke Hassan, ya ce dage dakatarwar jiragen saman kasashen duniya da Masarautar Saudi Arabiya ta yi, ya ba da babban fatan yiwuwar maniyyatan su tashi domin aikin Hajji da Umrah a bana.
Masarautar, a shekarar da ta gabata, ta dakatar da duk jirage na kasa da kasa da ke shigowa cikin kasar saboda annobar COVID-19, lamarin da ya haifar da mahajjata 1,000 ne kawai suka gudanar da aikin hajjin na shekarar 2020, wanda hakan ya rage yawan musulmai miliyan biyu da ke gudanar da aikin hajjin na shekara.
Ya tabbatar wa Musulmin Najeriya cewa da zaran masarautar ta sanar da sabbin ka’idoji kan aikin Hajji da Umrah, hukumar za ta dauki matakan da suka dace don amfanin maniyyatan.
“A halin yanzu, hukumar ta bukaci maniyyata, jihohi da sauran masu aikin hajji da Umrah masu lasisi da su ci gaba da shirye-shirye da rajista yayin da suke yin hakuri har sai Saudiyya ta bayar da cikakkun bayanai.”