2023: Magajin Buhari
Yankin kudu maso gabas ta kafe kan samar da shugaban kasa na gaba a 2023
A halin yanzu, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bi sahun wannan kira – Umahi ya bayyana cewa domin samar da zaman lafiya da hadin kai, ya kamata magajin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga yankin David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya shiga sahun masu ganin ya dace Shugaban kasa na gaba ya fito daga yankin arewa maso gabas.
Read Also:
Batun wanda zai karbi shugabanci daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 na ta daukar dumi inda kungiyoyi da mutane ke ta muhawara kan yankin da ya kamata a mikawa shugabancin. Da yake magana a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, Umahi, wanda ya kasance Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, ya bayyana cewa domin wanzar da adalci da kuma kare amincin kasa, ya kamata Shugaban kasa na gaba ya fito daga yankinsu.
Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa wannan shine kiran da matasan yankin ke yi, jaridar Punch ta ruwaito. Umahi ya kuma yaba ma jagororin zanga-zangar EndSARS kan ajiye komai a gefe tare da kawo karshen gangamin da suka yi a yankin kudu maso gabashin kasar.
Ya kuma yi Alla-wadai da harbe-harben Lekki sanan ya bayyana cewa gwamnonin kudu maso gabas za su ci gaba da kira ga “bincike domin hukunta masu laifin.” Gwamnan ya yi alkawarin daukar bukatun masu zanga-zangar zuwa gaban Shugaban kasa da kuma tabbatar da ganin cewa komai ya koma daidai.