Afghanistan: Mako ɗaya a Kasar Tamkar Zuwa Lahira a Dawo ne

 

  Ya ɗauki sa’o’i uku kafin Hussain Haidari ya sami abin da yake nema. Ya gane wa idanunsa fuskokin gawarwakin matasa da dama a cikin jakar saka gawarwakin kafin ya gano abin da yake nema, ɗan uwan matsarsa, Latif Sarwari.

   Shekarun Latif 20, kuma yana mataki na 12 a makarantar sakandare. Kamar sauran abokan karatunsa, ya koma birni Kabul watanni uku kacal da suka gabata don shirye-shiryen fara rubuta jarrabawar shiga jami’a.

  Barin sa cibiyar horarwa ta Kawsar-e-Danish a ranar Asabar, bayan halartar darasin sa’o’i huɗu da ya saba yi a kullum kenan, a daidai lokacin da dan harin kumar bakin waken ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

  Latif ya fito ne daga wani dan kauyen da ke lardin Ghazni, inda iyayensa da ke raye, ba su san mutuwar ɗan nasu ba.

  Hussain bai san hanyar da zai bi wajen sanar da iyayen Latif ba: ”Babu hanyar sadarwa a kauyen, da wane idon zamu tunkari mahaifiya da mahaifin tare da gawar ɗansu?

”Za mu ɗauki gawar Latif zuwa kauyen, inda ya bari don tafiya neman cimma burinsa, ba ya taras da ajalinsa ba.”

Iyayen Latif na daga cikin iyaye da ba su misaltuwa da ke cikin alhini sakamakon tashin hankalin da ke faruwa a Afghanistan, wanda duk da ana ci gaba da tattaunawar kawo zaman lafiya tsakanin mayaƙan Taliban da na gwamnatin Afghanstan ke ƙara ta’azzara.

An samu tafka ta’asa a ƙalla sau daya a kullum cikin makon da ya gabata a Afghanistan. BBC ta tattauna da wasu daga cikin mutanen da ke tsakiyar inda mummunan rikicin ke faruwa, kan ko shin yaya rayuwa take a cikin wannan yanayi.

Asabar 24 ga watan Oktobabirnin Kabul

Na kasa gane me yasa ake ta kashe su

Dalibai sun kai kimanin 600 a cibiyar horarwa ta Kawsar-e Danish, lokacin da ɗan harin ƙunar baƙin waken ya tarwatsa kansa. Mutum a ƙalla 25 ne – akasari ƙananan ɗalibai – suka hallaka, yayin da sauran 60 suka jikkata.

Tabish mai shekara 17 na daya daga cikin waɗanda suka tsira da ransu. Ya fita cikin sauri ne don samun horon ƙwallon ƙafa, wanda hakan ne ya ceci rayuwarsa.

“Ina daidai karshen kan layin ne lokacin da fashewar ta abku. Babban abokina, Mirwais Karimi – ɗalibi mai ƙwazo – ya hallaka, yana zaune kusa da ni a aji, na yi matuƙar kaɗuwa cewa yanzu ba ya tare da mu,” Tabish ya ce.

Mahaifin Tabish Fraidon Mohseni da farko bai san me ke faruwa ba game da fashewar.

“Lokacin misalin ƙarfe huɗu na yamma ne sai wani ya kira ni cewa in zo asibiti,” Fraidon ya ce. Da ya yi sauri ya fita, ya hangi motocin ɗaukar marasa lafiya a kan tituna, nan ne wasu munanan tunani suka fara zuwa masa a rai.

“Na samu ɗana da ransa, yana kwance kan gado – in ba don haka ba daga farko da na ɗauka ya mutu ne.”

Yanzu an sallami Tabish daga asibiti, amma lokacin da babansa ya ga raunukan da ke kai da kafafuwan ɗan nasa ya kasa dauriya.

Ya kasa gane me yasa ake kai hari kan ɗalibai. ” Karatu kawai suke son yi, kamar yadda Allah da Annabinsa suka umarta, na kasa gane me yasa ake kashe su.”

Kungiyar Taliban ta musanta hannu a kai wannan hari – a maimakon haka kungiyar IS ce ta yi ikirarin ƙaddamar da harin.

Akasarin ɗaliban da ke cibiyar ilmin sun fito ne daga yankin Hazara mabiya Shi’a, da ‘yan Sunni ”masu tsattsauran ra’ayi” ke ɗauka a matsayin masu saɓon Allah.

Akwai damuwar da ake yi cewa waɗannan hare-hare tsokana ce da ka iya rura wutar rikicin addini

Jumma’a 23 ga watan Oktoba lardin Nimruz

Sojoji a ƙalla 20 ne suka mutu a harin da ƙungiyar ta Taliban ta kai. Jami’an yankin sun tabbatar da cewa wasu da dama sun jikkata, yayin da aka yi garkuwa da sojoji shida.

An yi ta yaɗa hotunan gawarwakin sojojin a kafafen sada zumunta warwatse a cikin rairayin hamada, har ma da waɗanda aka yi garkuwa da su, waɗanda da alamu sun jikkata

Alhamis, 22 ga watan OktobaLardin Takhar 

Na bar gawar yarona a ƙasa don ceton wadanda suka jikkata’

“Yarana biyu suna cikin masallaci. Ɗaya ya hallaka, kuma yana wurin da aka kai hari ta sama – na kawo waɗanda suka ji rauni nan,” mahaifin ya ce.

Ƴaƴansa na ɗaukar darasin karatun Alkur’ani ne a cikin aji da ke masallacin, lokacin da jirgin yaƙin dakarun gwamnatin Afghanistan suka kai harin.”

Yara 12 suka hallaka, kana ƙarin wasu 18 da suka samu raunuka aka garzaya da su asibiti, tare da Abdul Wali, malamin da ke koyar da su a ajin.

Gwamnatin dai ta yi iƙirarin cewa ta yi niyyar kai harin ne kan yankin da mayaƙan Taliban suka fi ƙarfi.

Laraba 21 ga watan OktobaLardin Takhar

‘Na rasa sojojina…. ciki har da ɗana’

Hari ta sama a Lardin Takhar wani mayar da martani ne kan abin da ya faru a ranar da ta gabata, lokacin da mayaƙan na Taliban suka kai hari a sansanin dakarun musamman na ‘yan sandan Afghanistan.

Kwamandan rundunar ‘yan sandan Samangan Kanal Abdullah Gard, ya rasa ɗansa mai shekara 27, Farid. Har yanzu yana cikin kaɗuwa.

“Bai mutu ba, har yanzu ɗana yana da rai, ba zan manta da shi ba. Gurbinsa ba zai zama babu komai ba a zuƙatanmu ba,” Kanal Gard ya shaida wa BBC.

Farid ya gaji mahaifinsa.

“Ɗana ya samu ƙwarin gwiwa daga gare ni, ya shiga aikin ɗan sanda kuma, yayin da muke aiki iri ɗaya, ya zama tamkar abokina. Amma ba shi kaɗai na rasa ba: wasu daga cikin sojoji masu ƙwazo da suka mutu tare da shi.”

Laraba 21 ga watan Oktoba, Nangarhar

Matata ba ta son ni in fara mutuwa; amma yau na rasa ta

A ranar da aka kai harin Takhar, wasu munanan abubuwan sun ƙara faruwa a wasu sassa daban na Afghanistan.

Tashe-tashen hankulan sun tilasta wa ‘yan kasar ta Afghanistan da ɗana barin garuwansu, har ma da ƙasashensu, don samun mafaka, aiki ko kiwon lafiya.

A daidai lokacin da ga ‘yan kasar ta Afghanista rayuwa ta kasance a jiran ƙaddara, tashe-tashen hankulan suka ƙara ɗaukar salo daban-daban.

A birnin Jalalabad da ke gabashin kasar ta Afghanistan, fararen hula a ƙalla 15 ne da suka haɗa da mata 11 suka hallaka a yayin wani turmutsutsu lokacin da mutane ke bin layin neman takaradar biza.

Da sanyin wannan safiya ne, Niaz Mohammad mai shekara 60 ya dawo gida bayan aikin dare, sai ya fara lura da cewa matarsa ba ta nan.

Ta bar gida ne zuwa wajen bin layin neman biza da misalin ƙarfe biyu na dare don ta samu wuri mai kyau, saboda mutane masu neman takardar izinin shiga ƙasar Pakistan sun yi yawa, kuma an tara dubban takardun waɗanda suka rubuta neman takarar biza ɗin.

Ofishin hulɗar jakadancin kasar ta Pakistan ya sake buɗewa bayan shafe watanni takwas a rufe saboda annobar korona, don haka saboda taruwar takardun masu neman biza ɗin ya sa ta mayar da su zuwa filin wasan kwaloon kafa.

Kiran farko ne sai Niaz Mohammad ya samu labarin cewa mota ta kaɗe matarsa. Ya wuce kai tsaye zuwa asibiti – sai suka tura shi ɗakin ajiyar gawarwaki.

A can ne ya ga gawar matarsa Bibi Ziwar mai shekara 55.

Daga bisani ne ya samu labarin cewa mata bakwai ne suka faɗo a kan matar tasa, kuma duka sun mutu.

Bibi Ziwar ta mutu ta bar ƴaƴa maza takwas mata uku. Wasu daga cikinsu suna zaune ne a birnin Peshawar, a tsallaken kan iyaka da ƙasar Pakistan.

“Tana kewar jikokinta ne,” Mohammad ya shaida wa BBC. “Sun kasa zuwa wurin ta, kuma ta kasa daure nisan da suka yi da ita.”

Mohammad na kewar matarsa, kuma ba zai iya tuna maganarsu ta ƙarshe da ita ba.”

Kafin wannan rana ya fara rashin lafiya ne, sai ta ce ya daina aiki, a maimakon haka ya tura ‘ya’yansa su yi aikin nasa.

“Ba na so ka riga ni mutuwa,” ta ce, ” Idan ka fara mutuwa, ba mu san yadda za mu yi ba tare da kai ba. Amma idan na mutu, na san za ka kula da ‘ya’yanmu”

Talata 20 ga watan Oktoba, Lardunan Nimruz da Wardak

Sojoji a ƙalla biyar ne aka hallaka, yayin da biyu suka jikkata bayan da motocinsu sun ci karo da wata nakiya da aka dasa a bakin hanya a Lardin Nimruz.

Jagoran hukumar ‘yan sandan gundumar na daga cikin waɗanda suka mutu. Ƙarami ɗansa Benyamin ya bayyana a gidan talabijin a yankin yana cewa sai ya ɗauki fansa kan mayaƙan Taliban idan ya girma.

“Ina bayyana haka ne don Ashraf Ghani ya saurari bakin cikina. Mahaifina ya rasu saboda Ashraf Ghani don haka akwai buƙatar ya ji halin baƙin cikin da nake ciki.

”Daga bisani ne a ranar, bayan sa’o’i biyu da barin Birnin Kabul a Lardin Wardak wani bam da aka dasa ya samu motocin fararen hula 11.

Litinin 19 ga watan Oktoba, Khost da Urozgan

A Lardin Khost harin bam ya hallaka a ƙalla mutum huɗu, bayan tashin wasu ababen fashewa da ke ɗaure jikin wani babur a kusa da wurin da ake bikin aure, tare da jikkata sauran mutane 10.

A Lardin Urozgan, an hallaka wasu sojojin Afghanistan biyu, a wani harin ƙungiyar Taliban, yayin da huɗun suka jikkata.

Presentational grey line

Sunday 18 ga Oktoba, Lardin Ghor

Ni kurma ce, amma sai da na ji ƙarar tashin bam ɗin’

Razia, da ”yar uwarta Marzia da kuma ɗan uwanta Nayeb dukkaninsu kurame ne suna kuma halartar makarantar kurame a Lardin Ghor.

Ƴan gida dayan ba su jima da fara karatu a ajin nasu ba, inda suke wata duniyarsu da babu jin wani motsi, a daidai lokacin da wata motar ɗaukar kaya maƙare da ababan fashewa ta tarwatse a wajen ginin.

Mutane a ƙall 16 ne suka hallaka, kana fiye da 150 suka samu munanan raunuka. Fashewar ta lalata kewayen ginin da suka haɗa da makarantarsu.

“Shi ne karon farko a rayuwata da kunnena ya taɓa jin wani abu,” Razia, mai shekara 16 ta bayyana da alamun maganar kurame. ”Babbar ƙara ce, kunnuwana ba sa ji, ba kuma su saba jin duk wata ƙara ba, amma na ji wata babbar ƙara a kunnuwana.”

Razia, ta ce ‘yar uwarta da kuma ɗan uwanta suna cikin aji tare da sauran ɗalibai 19.

”Da farko na ɗauka na mutu ne. Ƴaruwata na motsi, amma na zaci shi ɗan uwana ya mutu – amma cikin sa’a ashe duk da ransu.”

Ga waɗanda ba sa ji ko kuma magana, kana suka faɗa cikin duhu, suka kuma tsira daga fashewar bam, wani halin ɗimauta ne mai tsanani da za a bayyana.

“Ni ma na ji, shi ne karon farko da na taɓa jin wani abu a kunnena, mai ƙarfin gaske ne, ƙara mai tsananin ƙarfin da ta girgiza zuciyata,” kamar yadda yayar Razia, Marzia ta bayyana.

Ƙaramin ɗakin karatun wanda ya kasance mafaka a gare su da wurin haɗuwa da abokansu, ya lalace.

Mako ɗaya bayan harin, Marzia ta murmure daga firgitar da ta yi, ta kuma je wurin mahaifiyarta don kwantar mata da hankali. Ta razana sosai da har ya sa ta ke tsoron sake fita daga cikin gida.

Razia da ‘yan uwanta sun taki sa’a, a ƙalla dai sun tsira da rayuwarsu. Amma a kusa da su akwai iyalai da suke ta alhinin rashin jigon gidajensu, suna kuma fuskantar matsalar rashin abinci.

Yawancin waɗanda harin bam ɗin motar ya shafa ma’aikata ne, cikinsu har da Abdul Hamid, wanda ya mutu ya bar ‘ya’ya mata biyar, maza uku da kuma mata daya

Matarsa Sayeda Bibi, ta ce sun tsere wa faɗan a ƙauyen mai nisa suka koma babban lardin a shekarar bara don neman mafaka.

“Mun bar komai a can, don tsira da rayukanmu, ka da a kashe mu. Ranar nan ya fita da sassafe amma bai sake dawowa ba. Yaran suna ta tambaya ta mene ne dalli, amma na kasa ba su amsa.”

Ta ce mijinta talaka ne, amma yana da ƙwazon nema, yana kuma tallafa wa iyalinsa. ”Ba mu da wani da zai taimaka mana, kana gwamnati ba ta tuntuɓe mu ba.”

Ƙarfin gwiwa da fatan ƙarshe’

Akwai alaƙa iri ɗaya da suke hade cikin duka waɗannan labarai: ɗalibai a birnin Kabul da suka yi bankwana da abokan karatunsu, uba da ɗa a Takhar sun rabu a fagen daga, iyalai da suka rabu da matsugunansu a Helmand sun rabu da dangi da kayansu, a Jalalabad, Bibi Zawir da jikokinta sun rabu a kan iyakoki biyu, da dai sauransu da dama da mutuwa da rayuwa ta raba su.

Labarun tashe-tashen hankula a Afghanistan na da tsawo. A makon da ya gabata kaɗai, mutane sun mutu a tashin hankali a sama da larduna 20 – a wasu an samu hare-hare har sau biyu a rana.

Idan dai ƙiyasin gwamnati na yawan fararen hula da suka mutu ko jikkata ya kasance mai wuyar tabbatarwa, to yawan na Taliban ka iya zama mafi wahala

Majalisar Ɗinkin Duniya a Afghanistan ta riga ta tattara bayanai cewa kimanin fararen hula 1,282 ne suka jikkata a farkon shekarar 2020 sakamakon tashin hankalin – yayin da kashi na biyu a cikin shekarar an shaida tashe-tashen hankula da ke ƙara ta’azzara.

Amurka ta rattaba hannun yarjejeniya da mayaƙan Taliban na ƙasar ta Afghanistan, kuma lokaci ya yi da za su janye sauran dakarunsu a farkon shekara mai zuwa.

Kana ƴan Taliban ɗin za su zauna a teburin tattauna wa da gwamnatin Afghanistan a ƙasar Qatar. Hakan ka iya zama muhimmin abu, amma mayaƙan Taliban ɗin sun karya alƙawarin nasu na janye kai hare-haren da suke yi.

Gwamnatin Afghanistan ta ce an tilasta mata sakin fursunonin Taliban 6,100 a wata alama ta mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar, amma haƙa ba ta cimma ruwa ba tun ma daga kan yarjejeniya wucin gadin.

Yawan waɗanda harin ya rutsa da su ya nuna yadda mayakan Taliban ɗin ke riƙon sakainar kashi ga yarjejeniyar zaman lafiyar, kana da gazawar gwamnatin Afghanistan wajen kare rayukan ‘yan ƙasarta.

Shaharzad Akbar jagorar hukumar kare hakkin bil adama mai zama kanta ta ofishin da ke tattara bayanai kan laifukan yaƙi a Afghanistan, kuma bayan makonnin da aka shafe na mummunan tashin hankali a faɗin Afghanistan ta wallafa saƙo a shafinta na Tuwita.

“Wannan labari ya mayar da hannun agogo baya wajen fatan da ake da shi. Abubuwa nawa za mu iya daurewa a matsayinmu na ƴan ƙasa? Har sau nawa za mu riƙa murmurewa? Za mu iya tashi kuwa?”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here