Abubuwa 12 Game da Sabon Shugaban Masu Rinjaye, Opeyemi Bamidele

Bayan tattake wuri kan neman manyan muƙamai a zauren Majalisar Dattawan Najeriya, an bayyana sunan Michael Opeyemi Bamidele a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya bayyana sunan Bamidele da mataimakinsa a ranar Talata, lokacin da majalisar ta dawo daga hutun makonni uku da ta tafi.

Michael Opeyemi Bamidele ɗan siyasa ne a matakin Majalisar Dattawa, wanda a halin yanzu yake wakiltar Ekiti ta tsakiya a majalisar ta tara.Michael Opeyemi Bamidele ɗan siyasa ne a matakin Majalisar Dattawa, wanda a halin yanzu yake wakiltar Ekiti ta tsakiya a majalisar ta tara.

Muhimman abubuwa 12 dangane da sabon shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa

1. An haifi Bamidele ne a garin Iyin Ekiti da ke jihar Ekiti a shekarar 1963. Sai dai Opeyemi ya girma ne a garin Legas, inda can ya gudanar da mafi yawancin rayuwarsa.

Bamidele ya sha gwagwarmaya gami da riƙe manyan muƙamai da dama a jihar ta Legas.

2. Opeyemi Bamidele ya yi karatunsa na sakandire a makarantar sakandiren Baptist Academy da ke Obanikoro cikin birnin Legas.

3. Bayan kammala sakandire, Bamidele ya wuce zuwa jami’ar Obapemi Awolowo da ke Ile-Ife ta jihar Osun, inda ya yi digirinsa na farko a jami’ar.

4. Bayan kammala digirinsa a jami’ar Ile-Ife, ya wuce zuwa jami’ar Benin da ke jihar Edo, inda ya yi digiri a ɓangaren shari’a.

5. Har ila yau, Bamidele ya zarce zuwa jami’ar Franklin Pierce da ke ƙasar Amurka, inda ya yi digiri na biyu a ɓangaren shari’a.

6. A shekarar 1992, Bamidele ya shiga zaɓen fitar da gwani na neman takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Oshodi/Isolo da ke jihar Legas, a ƙarƙashin jam’iyyar SDP inda ya sha kashi hannun abokin karawarsa.

7. Michael Opeyemi Bamidele ya yi aiki da Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake sanata, a matsayin mai taimaka masa kan harkokin shari’a.

8. A watan Yulin shekarar 2000, Tinubu ya naɗa Bamidele matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa da alaƙa tsakanin gwamnatoci a lokacin da yake gwamnan Legas.

9. A shekarar 2003, Tinubu ya naɗa Opeyemi kwamishinan matasa da wasanni da ci gaban zamantakewa na jihar Legas, muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 2007.

10. A watan Afrilun 2011, an zabi Opeyemi a matsayin ɗan Majalisar Wakilai don ya wakilci Ekiti ta tsakiya ta ɗaya, a zauren Majalisar Wakilai ta bakwai.

11. Bamidele ya yi takara a zaɓen gwamna na jihar Ekiti da ya gudana a shekarar 2014 ƙarƙashin jam’iyyar Labour, sai dai Bamidele ya sha kashi hannun Ayo Fayose.

12. A shekarar 2019 ne aka zaɓi Bamidele a matsayin sanata da ke wakiltar Ekiti ta tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here