Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa da Fasto a Kaduna

Wasu ƴan bindiga sun sace shugaban masu wa’azi a cocin Katolika na Holy Trinity da ke Karku a ƙaramar Hukumar Kauru da ke jihar Kaduna, Rabaran-fada Jeremiah Yakubu.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da daddare a gidansa da ke jikin mujami’ar.

A lokacin da ya tabbatar da faruwar lamarin, ɗaya daga cikin shugabannin Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab, ya ce cocin ta rubuta musu takarda inda ta sanar da su kan sace malamin kiristan.

Takardar ta buƙaci a yi addu’a domin ganin an ceto faston cikin ƙoshin lafiya.

Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da sace-sacen mutane da garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here