2020: Adadin Mutanen da Suka Mutu a Cutar Zazzabin Lassa – NCDC

Mutum 242 suka mutu daga cutar Zazzabin Lassa a shekarar 2020.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria ce ta fitar da hakan.

Cutar ta samo asali ne a wani gari a arewacin Nigeria inda aka fara gano.

ta Akalla mutum 242 ne suka rasa rayaukansu sanadiyyar cutar Zazzabin Lassa a shekarar nan a Nigeria.

Hakan na kunshe ne a wani rahoto da cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria ta saki kamar yadda The punch ta ruwaito.

Zazzabin Lassa cuta ce da take yaduwa a cikin mutane ta abinci ko kayan amfanin gida da kashin Bera ko fitsarinshi ya taba.

Cutar ta bazu a kasashen Afrika na yamma, kuma an samo asalin sunanta daga wani gari mai suna Lassa a arewacin Nigeria inda aka gano cutar a karon farko a shekarar 1969.

Kasashen da ta bazu sune- Sierra Leone, Liberia,Guinea da Nigeria. Sannan sauran kasashen dake makwabtaka dasu suna cikin hatsarinta.

Game da rahoton NCDC, Mutum 1175 ne suka kamu da cutar a Nigeria a shekarar 2020, sannan 817 ne suka kamu a shekarar 2019.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here