Jam’iyyar Adawa a Chadi ta Soki Tsawaita Mulkin Mahamat Deby
Babbar jam’iyyar adawa ta kasar Chadi ta bayyana rantsar da jagoran mulkin soji na kasar Mahamat Idriss Deby na karin shekara biyu a matsayin wata koma-baya ga mulkin demokradiyya.
Read Also:
Mataimakin shugaban kungiyar da ake kira “The Transformers”, masu neman kawo sauyi, Ndolembai Njesada, ya kuma soki damar da aka bai wa Mahamet Deby na yin takara a zaben kasar mai zuwa.
Ya bayyana cewa wannan tamkar an bai wa shugaban wuka da nama ne.
Mr Njesada ya kuma yi barazanar kafa gwamnati ta daban a kasar.
Manyan kungiyoyin ‘yan adawa na kasar da ‘yan tawaye sun ki shiga tattaunawar da aka gudanar, wadda a lokacin ne aka amince da tsawaita mulkin Shugaba Deby.
A bara ne Mahamat Deby ya karbi mulki bayan kisan da aka yi wa mahaifinsa a fagen daga.