Kaddamar da Aikin Ma’aikatar Jin Kai na Taswirar Hanya da Tsarin Ci gaban Kasa – OSINBAJO 

 

gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tsarin taswirar hanya na ma’aikatar ayyukan jin kai, magance annoba da bunkasa rayuwar jama’a yayi daidai da tsarin cigaban kasa,

Da yake jawabi a wajen kaddamar da tsare-tsare na ma’aikatar kula da jin kai da annoba da ci gaban al’umma na tarayya a fadar shugaban kasa, mai girma mataimakin shugaban kasa Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, wanda mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Mista Adeola Rahman Ipaye ya wakilta, Yace, Ma’aikatar ta hanyar taswirar tana ba da gudummawa ga daidaito da ci gaba a kowane fanni na gudanar da mulki.

Ya kara da cewa, taswirar hanyar ta samar da  Muhimmancin haɗin kai a fadin Tarayya, Jihohi, da Kananan Hukumomi, don haifar da canji me dorewa a ƙasar Nigeria”.

Acikin jawabin sa yace,  “kamar dukkannin tsare-tsare da shirye-shirye mun fahimci cewa ita kanta taswirar hanyar za ta yi tasiri kwarai da gaske kuma Gwamnatin Tarayya a shirye take da ta tallafawa shirin”.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su hada kai da ma’aikatar domin samun zaman lafiya a tsakanin al’umma.

A wani jawabi da mai girma ministar harkokin jin kai, kula da annoba da ci gaban al’umma, Sadiya Umar Farouq ke cewa, “domin aiwatar da umarnin shugaban kasa yadda ya kamata, Ma’aikatar ta tsara tare da samar da dabarar taswirar hanya don shekarar 2021 zuwa shekarar 2025, wanda zai jagoraci cika kudurin ma’aikatar”.

Ministar ta kara da cewa, “Tsarin taswirar zai taimaka wajen inganta rayuwar Al’umma, hakan yayi daidai  da gagarumin aikin da Ma’aikatar ke yi na sauke nauyin da ya rataya a wuyan ta, wanda  ke da muhimmanci ga tattalin arzikin kasa da kuma jin dadin ‘yan kasar,  sarrafa annoba, ba da amsa ga al’amuran jin kai da aiwatar da shirye-shiryen ci gaban zamantakewa.

Ma’aikatar tana da matsaya mai kyau na tunkarar batutuwa da yawa, wanda ya hada annoba, rashin daidaituwar zamantakewa, rashin wadataccen abinci, tare da rashin daidaiton samun ababen more rayuwa a tsakanin ‘yan kasa”.

Ministar ta ci gaba da cewa, “a cikin tsara mahimman bayanai guda 7 (bakwai) na taswirar Dabarun Hanya. mun yi nazari sosai a kan muhimman abubuwa guda tara (9) masu muhimmanci na ajandar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Shirin Farfado da Tattalin arziki da ci Gaba (ERGP) Shirin Raya Kasa wanda Shugaban kasa ya kaddamar  a ranar Laraba, 22 ga Disamba, 2021.

Daidaita ginshiƙan dabarun Ma’aikatar tare da waɗannan tsare tsare, masu aiki na tabbatar da cewa ma’aikatar da masu ruwa da tsaki suna aiki kan hanyar da ta dace don ci gaban tarayya.

1.  Haka kuma taswirar ta gabatar da aiwatarwa, sa ido, kimantawa, bita, da kuma hanyoyin bayar da rahoto da za a tura don tabbatar da samar da sakamako mai inganci.

Wadannan mahimman tsare tsare gami da ingantattun kayan aiki aiki za su bai wa ma’aikatar damar lura da ingancin aikin gami da auna aiwatar da taswirar a cikin shekaru biyar na 2021 zuwa 2025.

Haka kuma aiwatar da tsare-tsaren na taswirar hanyar, tare da karfafa bangarorin  gwamnatin tarayya, zai kuma jagorance mu wajen cimma wa’adin ma’aikatar, inganta rayuwar ‘yan Najeriya masu rauni da kuma tsara rayuwar kowa.

2.  An bayyana wa ma’aikatar rukunni guda bakwai (7) wanda suka hada da,

A) Ƙarfafa Manufofi da Tsarin Gudanarwa;

B) Gina Tsare-Tsaren Shaida don Faɗakarwa da Ba da Lamuni;

C) bunkasa Shirye-Shiryen fannin kimiya;

D) Haɓaka hanyoyin samun kudi

E) Tabbatar Da hadin kai da Abokan Hulɗa, da baiwa nakasassu dama.

F) Aiwatar da Tsare-tsaren Haɗin Kan Jama’a don Inganta Sadarwa da tsarin Mulki;

G) Gudanar da manufofin ci gaba Mai Dorewa (SDGs) da tsarin jama’a tareda shirye-shiryen zuba Jari.

“Mun ba da cikakkun bayanai game da kowane ginshiƙin dabarun samar da tushe, da bayyana mahimman tsare-tsaren ayyuka, da gano mahimman masu ruwa da tsaki,

Taswirar ta kara nuna ayyukan da dole ne a aiwatar a karkashin tsari  me kyau tareda, sa ido da tantance matakan kowace dabara.

An tsara taswirar a  tsanake tare da karkasa su zuwa kashi kashi kuma an bayyana dangantakar da ke tsakanin su a fili a cikin taswirar hanya”.

“Ana sa ran bayan kaddamar da aikin a yau, dukkan manufa, shirye-shirye, himma da ayyukan sassan mu da hukumomin mu, za a daidaita tare da Dabarun Taswirar Hanya, Za a kuma gudanar da tarukan bita da tsare-tsare  daidai da tsare-tsaren da aka sa a gaba da kuma lokutan da suka dace a dukkan sassan da hukumomin da ma’aikatar ke kula da su”.

Ministar ta ce wannan taswirar dabarun ya samo asali ne daga tuntubar juna da tattaunawa mai zurfi a ciki da wajen ma’aikatar da hukumominta tare da nuna jin dadin ta ga duk wadanda suka ba da gudummawa wajen bunkasa Taswirar Hanya.

Babban sakataren ma’aikatar Bashir Nura Alkali a jawabin bude taron ya bayyana cewa bayan kaddamar da taswirar hanya. Ma’aikatar za ta ci gaba da tafiyar da rayuwar Taswirar Hanya, shirya jerin horo da bita ga duk masu ruwa da tsaki.

Babban Sakataren ya kara da cewa,

“Anyi ƙokari matuƙa wajen hangen nesa da tsara waɗannan tabbatattun dabaru kuma yana da mahimmanci mu hada hannu don ganin an yi nasarar aiwatarwa”.

Taron yayi nasarar samun manyan baki kamar haka,  Wakilin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ministan yada labarai da al’adu, Ministan Kudi da Tsare-Tsaren kasafin kudi, Ministan ciniki da zuba jari, Karamin Minista, Ci gaban ma’adinai da karafa, Shugabannin Kwamitin Majalisu  kan Yaki da  Talauci, IDPs da yan gudun hijira, Wakilin Gwamnan Jihar Borno, Abokan Hulɗa da Masu Ba da Tallafi na Ƙasashen Duniya,  jami’an diflomasiyya, da sauransu.

Rhoda Ishaku Iliya

Mataimakin Darakta (Bayanai)

Fabrairu 14, 2022

PHOTO CAPTION

Na tara daga hannun hagu, wakilin mataimakin shugaban kasa, prof . YEMI OSINBAJO, Mataimakin shugaban ma’aikata wa shugaban kasa, ADEOLA RAHMAN IPAYE, Na goma daga hannun hagu, ministan ayyukan jin kai, magance annoba da bunkasa rayuwar jama’a, SADIYA UMAR FAROUQ, na takwas daga hagu, ministan yada labarai, ALHAJI LAI MUHAMMAD,  na takwas daga hannun dama, shugaban kwamiti yaka da magance talauci, ABDULLAHI BALARABE SALAME, babban sakatare na FMHADMSD, BASHIR NURA ALKALI, na uku daga hannun dama, daraktan shirye shiryen bincike da kididdiga, FMHADMSD, HAJARA AHMAD, da sauran su, ayayin gudanarda shirye shiryen kaddamar da taswirar hanya 2021-2025 a ranar 14 ga watan fabrairu a Abuja.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here