Gwamnatin Nijar ta Gamsu da Tsare-Tsare da Ayyukan da Gwamnatin Gwamna Ganduje ke yi Don Cigaban Matasa

Ministan Koyar da sana’o’i na Jamhuriyar Nijar, Kassoum Mamane Moctar, a ranar Talata ya ce kasarsa ta gamsu da tsare-tsare da ayyukan da gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ke yi don cigaban matasa.

Ministan ya ce nasarorin da gwamnatin na Kano ta samu a bangaren matasan yasa Nijar ta tura tawaga zuwa Kano domin yin nazari kan tsare-tsaren koyar da matasa sana’oi’.

Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa ta gano cewa cigaban matasa ne ginshikin cigaba da kawar da ayyukan laifi shi yasa ta mayar da hankali a bangaren.

Kano – Ministan Koyar da Sana’o’i na Jamhuriyar Nijar, Kassoum Mamane Moctar, a ranar Talata ya ce kasarsa ta gamsu da tsare-tsare da ayyukan da gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ke yi don cigaban matasa.

Ministan ya ce nasarorin da gwamnatin na Kano ta samu a bangaren matasan yasa Nijar ta tura tawaga zuwa Kano domin yin nazari kan tsare-tsaren koyar da matasa sana’oi’, rahoton The Punch.

Moctar ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata yayin da ya kai wa Gwamna Ganduje ziyara a gidan gwamnatin Kano.

Sanarwar da babban sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan Kano, Hassan Musa Fagge, ya fitar ta ce Ministan ya kara da cewa tsare-tsaren na cigaban matasa da gwamnatin Kano ta fitar abin koyi ne.

Martanin Ganduje

A bangarensa, Gwamna Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce gwamnatin jihar ta gano cigaban matasa shine ginshikin cigaba hakan yasa ta ke bawa tsare-tsaren matasan muhimmanci.

A cewarsa:

“Tallafawa matasa yana da matukar muhimmanci domin yana hana zaman kashe wando da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuka.”

Gwamnan ya bawa tawagar ta Nijar tabbacin cigaba da hadin kai da goyon baya, yana mai cewa ziyarar da suka kai cibiyoyin tallafawa matasan shaida ne da ke nuna hadin gwiwa da ke tsakanin Najeriya da Nijar musamman Jihar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here