Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari Ta Kalubalanci Gwamnatinsu Da Wakar Adam Zango

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta shiga jerin masu fafutukar ganin an magance matsalar tsaro a yankin Arewacin kasar.

Hajiya Aisha Buhari, uwargidan shugaban Najeriya ta shiga jerin masu fafutukar ganin an magance matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewacin kasar, bayan da ta wallafa wani sako a shafin Twitter wanda masu lura da al’amura ke ganin kalubale ne ga gwamnatin shugaba Buhari.

Aisha ta wallafa wani dan gajeren bidiyo mai tsawon dakika 22 a karshen mako nan, inda ta rubuta mau’du’in #Achechijama’a, bidiyon da aka hada dauke da sabuwar wakar fitaccen jarumi kuma mawaki Adam A. Zango mai taken “Arewa Na Kuka”.
Wasu da dama na kallon sakon na Aisha a matsayin kalubale ga gwamnatin shugaba Buhari. Bidiyon ya nuna hotonun Buhari da hafsoshin sojin kasa suna taruka a lokuta daban-daban, wasu kuma an nuna shugaban a taron majalisar zartarwar kasar yayin da sautin wakar ta Zango ke bugawa a bayan fagen bidiyon.

​A gefe guda kuma wasu na ganin tana nuna yadda hukumomin kasar ke kokarin nemarwa kasar maslaha.

A lokacin hada wannan rahoto, mutum dubu 421 suka kalli sakon bidiyon a shafin uwargidan shugaban kasar, mutum 5,499 suka yi tsokaci, dubu 13.14 suka sake wallafa sakon, sannan dubu 16.6 suka nuna kaunarsu.

A karshen makon nan Zango ya fitar da wakar wacce ke dauke da baitukan neman hukumomi su kai wa yankin Arewacin kasar dauki.

“Arewa na kuka, ana zubar da jininmu, ana kashe al’umarmu, don Allah a kare mu, don Allah a tausaya.” Amshin wakar ta Zango mai tsawon minti uku da dakika biyu take cewa, wacce ya wallafa a shafinsa na Youtube a karshen makon nan.

Har mutum dubu 29 sun kalli wakar a shafin na Youtube cikin kwana biyu a dai-dai lokacin hada wannan rahoto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here