Yanzu Mun ga Amfanin Matakan da Gwamnatin Kaduna ke ɗauka da Zummar Daƙile Ayyukan ‘Yan Bindiga Masu Garkuwa da Mutane – Sarkin Birnin Gwari

 

Sarkin Birnin Gwari da ke Jahar Kaduna a arewacin Najeriya ya ce zuwa yanzu sun ga amfanin matakan da gwamnatin jahar ke ɗauka da zummar daƙile ayyukan ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya bayyana cewa matakan sun takure ‘yan bindigar, abin da ya sa yanzu suke neman abinci daga wajen mutanen da suka sace maimakon kuɗin fansa.

Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin taron ƙaddamar da rahoto kan matsalar tsaro da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta jahar ta gabatar wa Gwamna Nasir El-Rufai.

“Mun nuna cewa matakan da gwamnati ta ɗauka na toshe layukan salula da hana hawan mashin da hana sayar da man fetur a ko’ina ya yi amfani ƙwarai da gaske domin mun gani a wajenmu kuma muna da labarin sauran wurare,” in ji shi.

“Waɗannan matakai sun takura su ta yadda idan suka saci mutane sai dai su ce a ba su abinci ba kuɗi ba.

Muna goyon bayan gwamnati kuma muna addu’ar Allah ya kawo ƙarshen wannan abu.”

Rahoton ya duba rikice-rikicen da suka faru na ‘yan fashin daji da ƙabilanci daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021.

Mutum 343 aka kashe sannan aka saci 830 tare da jikkata 210 jumilla sakamakon tashe-tashen hankalin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here