Bidiyon Baɗala: Benzema ya Gurfana a Kotu

Daya daga cikin fitatttun ‘yan wasan kwallon kafa na Turai, wanda kuma ke taka leda a Faransa da Real Madrid Karim Benzema, ya gurfana a gaban wata kotu da ke wajan birnin Paris.

Ana tuhumarsa da da hadin baki a kokarin karbar kudi daga hannun tsohon dan wasan Faransa Mathiue Valbuena kan wani bidiyon baɗala.

Bezema ya jadada cewa ba shi da alaka da yunkurin karbar kudin amma ya shirya wata ganawa tsakanin abokinsa da dan wasan domin bayar da shawara kan abin da ya kamata ya yi domin ya fitar da kansa daga abin kunya.

Wani kwararre kan komfuta a birnin Marseille ya samu wani hoton bidiyo da ya nuna Valbuena yana jima’i da wata mace kuma ya yi kokarin karbar kudi daga hannunsa kafin ya goge bidiyon.

Dan wasan zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara biyar da kuma tarar kudi mai yawa idan aka same shi da laifi.

Dan wasan zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara biyar da kuma tarar kudi mai yawa idan aka same shi da laifi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here