ƙasar Amurka ta Cire Kuɗaɗen Biza ga ƴan Najeriya

 

Gwamnatin Amurka ta yafe biyan kudin biza ga ‘yan Nigeria ma su sha’awar ziyartar kasar.

Ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta ce cire kudin ya biyo bayan ragi da cire kudin daukan hoton zanen yatsa da FG ta yi wa Amurkawa ma su son zuwa Nigeria.

A cewar ma’aikatar, ma su sha’awar ziyartar kasar Amurka za su iya ziyartar shafin yanar gizo www.travel.state.gov domin karin bayani.

Gwamnatin ƙasar Amurka ta sauke nauyin biyan kuɗin biza ga dukkan ƴan ƙasar Najeriya kuma tsarin zai fara aiki daga ranar 3 ga watan Disamba 2020, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa ranar Asabar.

Kamar yadda bayanai suka nuna daga ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Amurka, ta cikin wata sanarwa da kakakinta, Ferdinand Nwonye, ya fitar ranar Asabar, ta yi bayani kamar haka;

“Ma’aikatar harkokin waje na sanar da cewa gwamnatin ƙasar Amurka ta cire kuɗaɗen biza ga ƴan Najeriya masu buƙatar bizar ƙasar Amurka.

“Wannan cigaba ya zo ne a matsayin godiya bisa tsarin rage adadin yawan kudin biza da kuma kuɗin ɗaukar zanen yatsu da ƴan ƙasar Amurka masu buƙatar bizar Najeriya ke biya wanda gwamnatin Najeriya ta yi.”

“Saboda haka, gwamnatin ƙasar Amurka ta soke kuɗaɗen bizar shigowa ƙasar Amurka ga ƴan Najeriya daga ranar 2 ga watan Disamba.”

“Ga duk Ƴan Najeriya masu buƙatar tafiya ƙasar Amurka, ana shawartar su da su ziyarci adireshin yanar gizo www.travel.state.gov don samun ƙarin bayanai,” a cewar sanarwa da hukumar ta wallafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here