Amurka ta Gano Jemagun da ke Bai wa Juna Tazara Idan ba su da Lafiya

Wani sabon bincike ya nuna cewa jemagu kan yi nesa da junansu a lokacin da suka kamu da rashin lafiya, yayin da sukan takaita yadda suke mu’amala a kusa da junansu da kuma takaita yawan adadin wadanda za su rika mu’amala da su.

An gano wannan halayya ne a cikin dakin bincike, amma kuma masana kimiyya sun gudanar da binciken ne kan wasu jemagun daji masu shan jini a kasar Belize da ke yankin tsakiyar Amurka.

Masana kimiyyar a jami’ar jihar Ohio ta Amurka, sun wallafa binciken nasu a mujallar nazarin halayyar yanayin kasa,

Sun bi diddigin wasu jemagu da ke rayuwa a wani kogon bishiya, bayan da suka makala wasu kananan na’urorin daukar hoto, don gano yadda suke mu’amala da juna.

A wani bangare na wannan bincike, masanan sun yi wa jemagun allurar wani sinadari da ake kira lipopolysaccharide, da ya saka garkuwar jikinsu ta kasance tamkar sun kamu da rashin lafiya, don gano ko halayyarsu za ta sauya.

Gabaki daya, jemagu 31 da daya ne, yayin da sauran jemagun aka yi musu nau’in allurar da ba zata taba garkuwar jikin na su ba.

Masu binciken sun ce babu ko da daya daga cikin jemagun da ya samu cutarwa a lokacin binciken.

Takaita yin mu’amala da juna

Masana sun gano cewa ‘jemagu marasa lafiya,’wadanda aka jirkita garkuwar jikinsu, sun kaurace wa jemagu ‘yan uwansu fiye da wadanda ke cikin koshin lafiya.

Ba su yarda su yi mu’amala da sauran jemagun ba, sun kuma takaita zirga-zirga kana suna nuna alamun jin barci fiye da sauran.

Wannan banbancin halayya ya ragu cikin sa’oi shida da yi musu allurar, kana a lokacin da jemagun ke barci ko kuma suka fita neman abinci.

Bayan sa’oi 48, karfin allurar ya sake su gabaki daya, kuma jemagun sun ci gaba da yin mu’amala tare kamar yadda suka saba.

A lokacin da suka fara rashin lafiya, da wuya jemagun su yada wata kwayar cuta a cikin daji saboda sukan yi nesa da jemagun da ke da koshin lafiya.

Jagoran binciken, Simon Ripperger, ya yi wa wannan lakabi da ‘ kaurace mu’amala da juna na dole’ tare da yin amanna cewa irin wannan halayya ka iya fadada a tsakanin sauran dabbobin dajin fiye da yadda muke tsammani.

Kasancewa a kan gado

“Na’urorin sun kara mana basira kan yadda halayyar mu’amaalar jemagu kan sauya da sa’a zuwa sa’a, har ma daga minti zuwa minti a lokutan dare da rana, da ma lokacin da suke boye cikin duhuwar kogon bishiya, ” in ji Simon Ripperger daga jami’ar Ohio .

Kauracewa juna na dole zai yi kyau ga mutanen da suka ji ba sa jin dadin jikinsu su kasance kwance a gado, fiye da kasancewa a cikin jama’a.

Wannnan halayya na da amfani ga lafiyar dabbobin daji da ke tare wuri guda saboda hakan ka iya hana yaduwar cututtuka a tsakaninsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here