An ga Watan Ramadana na Shekarar 1442 AH, Gobe Azumi – Sarkin Musulmai
Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa an ga jinjirin watan Ramadana a wurare daban-daban a Najeriya, mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar.
Hakazalika Kwamitin neman wata a Najeriya ce tayi wannan sanarwa a shafinta na Tuwita.
A jawabin da yayi kai tsaye, Sarkin Musulmi ya ce an ga watan Ramadana na shekarar 1442 AH.
Ya yi kira ga Musulmai su fara azuni kuma su koma ga Allah lokacin wannan wata mai alfarma.
Read Also:
Ya bukacesu su roki Allah ya kawo karshen matsalar tsaro da annobar Korona a Najeriya.
Sultan ya yi addu’an cewa Allah ya baiwa Musulami daman gabatar da ibadunsu kuma ya yi kira ga Musulman su bi dokokin da aka gindaya na kariya daga annobar corona.
A jawabin da majalisar koli ta sharia’ar Musulunci a Najeriya NSCIA ta saki, tace:
“NSCIA karkashin jagorancin shugabanta kuma Sultan na Sokoto na sanar da daukacin al’ummar Musulmi cewa an ga jinjirin watan Ramadana a yau 12/04/2021 wanda yayi daidai da 29 Sha’aban. 1442AH.
“Saboda haka gobe, 13 ga Afrilu, 2021 ne 1 ga watan Ramadan 1442AH.”