Samar da Danyen Mai: Angola da Libya Sun Shiga Gaban Najeriya – OPEC
Adadin danyen man fetur da Najeriya ke samarwa ya yi kasa zuwa ganga 972,000 a duk rana a cikin watan Agusta, wanda hakan yasa kasashen Angola da Libya suka shiga gabanta wurin samar da danyen man a watan.
Read Also:
Hakan na kunshe ne a rahoton da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) ta fitar a cikin watan Satumba.
Wannan ne karon farko a cikin shekaru da dama, da Najeriya ta samar da ganga kasa da miliyan daya ta danyen man fetur a rana.
Kazalika rahoton na OPEC ya ce lamarin ya sa kasashen Angola da Libya sun sauko da Najeriya wurin samar da danyen man fetur a dan tsakanin.
Rahoton ya ce ” fitar da danyen mai ya karu a kasashen Libya da Saudi Arabia, yayin da ya ragu a Najeriya.”