Ambaliyar Ruwa: An ‘Dage Bude Makarantu a Sudan

 

Gwamnatin Sudan ta sanar da dage bude makarantu a fadin kasar, saboda ambaliya da ta daidaita yankuna da dama a kasar.

Da ma a wannan watan ya kamata a fara sabon zangon karatu a kasar, to amma yanzu an dage batun komawar har sai ranar 2 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridun cikin gida suka ambato Ministan Ilimi Sir al-Khatim al-Huri yana fada.

Akalla makarantu 623 ne ambaliyar ta shafa, kuma an dauki matakin ne da nufin gyara su kafin a cigaba da karatu.

Ruwan sama mai karfi da ambaliya sun kashe sama da mutum 100, tare da lalata dubban gidaje a gwamman jihohin Sudan a makonnin da suka wuce

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here