Gwamnatina ta yi Namijin Kokari – Shugaba Buhari

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi namijin kokari, idan aka yi la’akari da dan abin da take samu wurin tafiyar da lamuran kasar.

Shugaban ya yi kalaman ne yayin da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar Imo da ke birnin Owerri ranar Talata, bayan bude wasu manyan ayyuka da Gwamna Hope Uzodinma ya yi.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin gudanar da ayyuka da dama duk da kudaden da take samu ba basu isa.

”Wannan gwamnati ta yi kokari sosai. Dole na fada saboda wadanda alhakin fadar hakan ya rataya a wuyansu ba sa yin haka. Ban san me ya sa ba,” in ji Shugaba Buhari.

Ya kuma jinjina wa gwamnatinsa bisa nasarar da ta samu na gurgunta kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a Kudu maso Gabas, a rikicin da ya ce ya gada daga gwamnatin PDP a 2015.

Shugaban ya kuma yi jinjina ga gwamnan jihar ta Imo kan gayyatar shi a karo na biyu cikin shekara daya don ya bude ayyukan da ya aiwatar

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here