Batanci ga Shugaba Buhari: Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta yi wa Mambobin APC 5 na Jahar Adamawa Tambayoyi

 

Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya, DSS, ta yi wa tsohon gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow tambayoyi kan halartar taron batanci ga Buhari.

An ce Bindow ya kasance a wurin wani taro inda wasu ‘yan jam’iyyar APC suka yi mugun fata ga Shugaba Buhari.

DSS ta kuma yi wa wasu mambobin APC biyar da suka halarci taron tambayoyi.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa Jibrilla Bindow, tsohon gwamnan jahar Adamawa tambayoyi a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, jaridar TheCable ta ruwaito.

Sadiq Abdullateef, hadimin tsohon gwamnan, ya shaidawa jaridar cewa Bindow ya amsa gayyatar hukumar DSS kuma an sake shi.

A cewar jaridar, ‘yan sandan sirri sun yi hira da Bindow tare da wasu mutane biyar, da suka hada da:

1. Kabiru Mijinyawa, tsohon kakakin majalisar dokokin Adamawa

2. Sulaiman Adamu, shugaban riko na jam’iyyar APC Yola ta kudu

3. Mustapha Barkindo, tsohon mai ba da shawara a lokacin gwamnatin Bindow

4. Abubakar Umar Sirimbai, tsohon kwamishina

5. Yusha’u Adamu

An tattaro cewa tsohon gwamnan ya yi wani taron jam’iyya a Adamawa inda wasu fusatattun mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka yi batanci ga Shugaba Muhammadu Buhari.

An fitar da wan faifan ganawar ga manema labarai, kuma an ce wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun yi fatan mutuwa ga shugaban kasar.

Hukumar DSS ta gayyaci manyan mahalarta taron don yi masu tambayoyi a kan faifan sauti da aka fallasa.

Bindow ya yi Allah wadai da masu kalaman batancin kan Buhari

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Abdullateef ya ce tsohon gwamnan ya yi Allah wadai da masu kalaman batanci ga shugaban kasar a taron.

Sanarwar ta ce:

“An gayyaci tsohon gwamnan jahar Adamawa, Sanata Muhammad Umar Jibrilla Bindow zuwa taron jam’iyyar saboda wasu mambobin jam’iyyar sun fusata game da zaben fidda gwani da aka kammala, wanda ya halarta a matsayin dattijon jam’iyyar.”

“Ya cancanci a lura cewa, babu wani shiri a cikin taron da aka ce, ya je can ya zauna ya saurari korafe -korafen mambobin, kuma akwai furuci da ba daidai ba daga wasu membobi wanda ya yi gargadi, abin bakin ciki ne cewa wasu mutane suna amfani da wanda ya harzuka tare da nadir murya don cin mutuncin tsohon gwamnan.

“Shiri ne wannan muryar da aka nada kuma idan kun saurare shi sosai, akwai wasu maganganun da aka tsallake, Sanata Bindow ya gargadi membobin da ke yin waɗannan maganganun marasa inganci sau uku a cikin taron har ma da barazanar ficewa.

“Kalamansa sun kasance, ‘Don Allah wannan bai dace ba, ba a yi wa wani fatan mutuwa saboda dalilai na siyasa, ku takaita magana game da shugabanmu kuma uba, shugaban kasa. Ku bari mu ci gaba don Allah, ko na tafi ‘.

“Amma saboda an shirya abun don yin ɓatanci da haifar da matsaloli ainda babu ne, maganganunsa na yin Allah wadai da abin da aka faɗi ba ma ya cikin faifan da aka watsa.

“Shugaba Muhammadu Buhari tamkar uba ne ga Bindow kuma ba zai taba jin dadin irin wannan a kan shugaban kasar ba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here