Mun Tafka Mummunar Asara Mai Yawa a Yaƙin da mu ka ƙaddamar a Ukaraine – Rasha
Rasha ta yarda cewa ta “mummunan asara kuma mai yawa” a yaƙin da ta ƙaddamar a Ukaraine, yayin da mamayar ke shiga kwana na 44.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa ta Kremlin, Dmitry Peskov, ya faɗa kafar talabijin ta Sky News cewa asarar da suka yi “babban bala’i ne gare mu”.
Ya ce yana fatan “nan da ‘yan kwanaki Rasha za ta cimma muradinta”.
Read Also:
Yanzu dai Rasha ta janye dakarunta daga yankin birnin Kyiv sannan ta mayar da yaƙi kan gabashin Ukraine – amma babu alamun tsagaita yaƙin.
A ranar 25 ga watan Maris Ma’aikatar Tsaro ta Rasha ta ce an kashe sojojinta 1,351 a yaƙin, amma Ukraine na cewa sun kai 19,000. Sai dai ba za a iya tabbatar da haƙiƙanin adadin ba saboda Rasha ka iya ragewa, Ukraine kuma ka iya ƙarawa.
Kalaman Mista Peskov na zuwa ne kwana ɗaya bayan korar Rashar daga Majalisar Kare Haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).