Shugaba Buhari ya Nemi Majalisa ta ƙara Yawan Kuɗin Tallafin Man Fetur na Kasafin Kuɗin 2022

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi majalisar tarayyar ƙasar ta ƙara yawan kuɗin tallafin man fetur na kasafin kuɗin 2022 daga biliyan 442 zuwa tiriliyan huɗu.

Buhari ya buƙaci hakan ne cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa ‘yan majalisar, inda yake neman su yi wa dokar kasafin kuɗin gyara.

Cikin wasiƙar wadda Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajamila ya karanta a zaman majalisa na ranar Alhamis, Buhari ya ambaci hauhawar farashin ɗanyen man fetur sakamakon yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine.

“Kamar yadda kuka sani, an samu sauyi a tattalin arziƙin duniya da kuma na cikin gida wanda ya tilasta neman gyara kan Tafarkin Harkokin Kuɗi na 2022 wanda aka gina kasafin kuɗi na 2022 a kansa,” a cewar Buhari.

A cewarsa, sauyin da za a samu a tafarkin ya haɗa da ƙari a kan hasashen farashin ɗanyen mai daga dala 62 zuwa 73 a kan kowace ganga da aka saka a kasafin kuɗin na 2022.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here