Tsohon Shugaban Hukumar Zabe, Attahiru Jega ya Koma Jam’iyyar PRP
Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ya koma jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP).
Wa’adin Jega a matsayin shugaban INEC ya ƙare a ranar 30 ga Yuni, yan watanni bayan ya gudanar da zaɓen 2015.
A cewarsa, duka jam’iyyun APC da PDP mai mulki sun gazawa yan Najeriya.
Kaduna, Kaduna – Shekaru shida bayan karewar wa’adin mulkinsa a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya sanar da matakinsa na yin siyasar bangaranci gabanin babban zaben 2023.
Read Also:
The News ta rahoto cewa Jega ya koma jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) sabanin hasashen da wasu bangarorin suka yi na cewa farfesa na iya hadewa da jam’iyyar All Progress Congress (APC) mai mulki.
Legit.ng ta tattaro cewa yayin bayar da dalilinsa na zabar PRP, ya ce saboda manyan jam’iyyun biyu – All progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) ba su cika muradin ‘yan Najeriya ba.
Jega ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su watsar da jam’iyyun biyu saboda mugayen halayensu a cikin shekaru 20 da suka gabata.
Jaridar ThisDay ta kuma ruwaito cewa Jega ya bayyana zama memba na sabuwar jam’iyyar siyasa, PRP kuma ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su zabi APC da PDP a zaben 2023.
Sai dai, ya lura cewa karuwar amfani da fasaha shine mafi kyawun aiki a duniya don inganta amincin zaɓe.