‘Yan Banga Sun Bindige Masu Garkuwa da Mutane a Jahar Taraba

 

‘Yan banga sun bindige wasu masu garkuwa da mutane a yayin da suka zo karbar kudin fansa.

Masu garkuwar sun sace wani dattijo ne kuma suka umurci yan uwan su kawo kudin domin fansarsa.

Sai dai kafin su tafi kai kudin, yan uwan dattijon sun sanar da yan banga wanda su kuma suka yi wa masu garkuwar kwantar bauna suka bindige su.

Gassol, Jahar Taraba – An bindige wasu masu garkuwa da mutane biyu har lahira yayin da suka zo karbar kudin fansa a garin Sabon gida da ke karamar hukumar Gassol na jahar Taraba.

Daily Trust ta gano cewa wadanda ake zargin sun sace wani dattijo ne mai suna Alhaji Gambo.

Wadanda ake zargi da garkuwar masu suna Sani da Musa sun umurci iyalan wanda suka sace din su kawo kudin fansar zuwa wani wuri.

Yadda yan bangan suka shirya wa masu garkuwar harin kwantar bauna.

Daily Trust ta ruwaito cewa an sanar da yan banga da ke yankin kuma suka tafi wurin domin yi wa masu garkuwar kwantar bauna.

Masu garkuwan sun tawo da makamansu, amma ba su san cewa yan bangan suna wurin ba kuma suka bindige su a lokacin da suke kwashe kudaden.

An ceto dattijon da suka kawo shi wurin da za su karba kudin fansa. Wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwar da aka kashe sun halaka mutane da dama a kauyukan Borno-Korokoro,Tella, Sabongida, Dananacha da wasu kauyuka da ke hanyar Jalingo zuwa Wukari duk a jahar Taraba.

Rundunar yan sandan Taraba ta tabbatarda kashe masu garkuwar Mai magana da yawun yan sandan jahar Taraba, ASP Abdullahi Usman, ya tabbatar da kashe masu garkuwan amma bai yi karin bayani ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here