Shehu Sani ya Bayyana Yadda ‘Yan kungiyar IPOB Suka fi ‘Yan Bindiga Hatsari

Tsohon Sanata ya bayyana yadda yan bindiga suka fi IPOB da Igboho hatsari.

Ya fadi haka ne a wata tattaunawa da yan Jarida.

Ya kuma yabawa gwamnatin Kaduna kan wanke Sheikh Ibrahim El Zakzaky da matarsa.

Shehu Sani, Tsohon sanata wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisa ta takwas kuma tsohon ciyaman a Kwamitin basussuka na gida da waje ya nuna yadda yan bindiga suka fi IPOB da Igboho hatsari.

A wata tattaunawa da Jaridar The Sun tsohon sanatan ya bayyana cewa da lokacin da gwamnatin tarayya take batawa wurin yakar yan aware, shi tayi amfani da shi wurin yakar yan ta’adda toh da an samu sukuni da tsaro arewa maso gabashin kasar.

Ga abinda yace game da aikin yan bindiga

“Jihar Kaduna a kewaye take da ayyukan yan bindiga, suna talauta mutanenmu wanda hakan yake tilasta musu saida gidajensu, filaye da wasu kadarori domin kawai su biya kudin fansan yanuwansu da aka sace.

Sun lalata tsarin noma wanda hakan yasa manona basa iya zuwa gonakinsu.

Tsarin Ilimi duk ya lalace saboda zaluncin wadannan mutane.

Har lalacewar ta kai suna karban haraji a wasu wurare.

Sun riga sun zama jaha a cikin jaha, Wannan shine abin bakin .cikin da muka tsinci kanmu a yau Garkuwa da mutane ya zama sana’a a Arewa ta yamma a kasarnan, sun riga sun zama shugabannin kansu.

A jaharmu Kaduna, ba ranar Allah da zata fadi da bazaka a ruwaito anyi garkuwa da mutane ba.

Sai anyi garkuwar mai yawa ma kake ji ba na uku ko mutum hudu ba.idan suka sace mutum, sannan aka ki biyan kudin fansa kan lokaci sai su siyar da mutumin ga wasu masu garkuwar wanda zai kara kudin fansan da za’a biya.

Ya kamata gwamnati ta rika tattaunawa da yan bindigan nan, ta haka ne kawai zamu kawo karshen matsalar nan.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here