Ra’ayoyin Ƴan Najeriya Game da Umarnin CBN na Ci gaba da Amfani da Tsofaffin Takardun Kuɗi

 

Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu game da sabon umarnin Babban Bankin ƙasar CBN na cewa al’umma na iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 200, da 500 da kuma 1,000.

A ranar Litinin ne CBN ya fitar da sanarwa ɗauke da umarnin kuma tun lokacin jama’a suke ta tsokaci game da al’amarin.

Batun sauya fasalin takardun kuɗi a Najeriya mataki ne da ya janyo cece-kuce tun bayan da gwamnati ta soma aiwatar da shi har ta kai wasu jihohi 16 sun ƙalubalanci matakin a Kotun Ƙoli.

Kotun Ƙolin dai a ƙarshe ta yanke cewa a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin har zuwa 31 ga watan Disamba sai dai tun bayan wannan umarni, gwamnati da shi CBN suka yi gum ba su ce komai a kan lamarin ba.

Sai dai a baya-bayan nan ne Shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari ya fito ya ce ko kusa bai taɓa neman CBN ko atoni janar na ƙasar su ƙi martaba umarnin kotun ba.

Kuma bayan Shugaba Buharin ya yi wannan furuci ne CBN ya fitar da sanarwar cewar mutane su ci gaba da amfani da kuɗaɗen kamar yadda Kotun Ƙolin ta bayar da umarni a hukuncinta.

Mutane da dama na ta bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta. Mun tsakuro muku daga shafukanmu.

Jibrin Ibrahim, wani masananin harkokin siyasa kuma wakili a Cibiyar haɓaka dimokraɗiyya CDD ya ce “bayan shafe watanni ƴan Najeriya na shan wahala, Shugaba Buhari da CBN sun amince da umarnin Kotun Ƙoli ba tare da neman afuwar ƴan ƙasa ba kan yin watsi da dokar.

Shi kuwa, Dipo Awojide a shafin na Tuwita cewa ya yi “A ƙarshe dai Gwamna El-Rufai da Gwamna Yahaya Bello na Kogi da sauran gwamnonin da suka ƙalubalanci CBN sun yi nasara, amma dai mai faruwa ta faru. An kai wa bankuna hari. An farfasa na’urorin cirar kuɗi na ATM. An samu tashin hankali a wasu jihohi ƙalilan.”

Aisha Abubakar wata malama ce da ke amfani da shafin na Tuwita inda kuma ta yi tsokaci da cewa “Duk da cewa CBN ya ba da kai ga umarnin Kotun Ƙoli, ina fargabar za mu ci gaba da shan wahala wajen samun kuɗi saboda ba duka kuɗaɗen da aka karɓa ba za a sake mayar da su domin ci gaba da hada-hada da su”.

Shi ma Gimba Kakanda, wani fitacce ne s shafin Tuwita. Ya dai mayar da martani ne kan saƙon da CBN ya wallafa na sanar da sabon umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin inda Gimba ya yi martani da cewa “Suna ina? – ma’ana a ina kuɗaɗen suke?

A na shi ɓangaren, Sanusi Dantata wasu tambayoyi ya jero game da batun

1. Shin za a riƙa samun tsofaffin takardun kuɗin?

2. Me tsarin da bai yi nasara ba ya cimma?

3. Wa ya kamata ya biya ƴan Najeriya kan wahalhalun da suka jurewa?

Bankuna da kasuwanni a jihar Kano sun fara da hada-hada da sabbin takardun kuɗi na naira dubu ɗaya da kuma ɗari biyar.

Wakilin BBC da ya zagaya wasu kasuwanni ya ruwaito cewa Jama’a na ta hada-hada wasu na shigar da kuɗi wasu kuma na karɓar kuɗaɗen akasari kuma tsaffin takardun kuɗi ne na dubu ɗaya da kuma ɗari biyar.

Wani da BBC ta yi hira da shi ya ce “na zo banki karɓar kuɗi, na yi farin ciki na zo na ga ana bayar da tsofaffin kuɗi, kuma na karɓa na yi murna, da ba za a karɓa ba, banki ba za su bayar da tsofaffin kuɗi ba.”

Haka ma lamarin yake a wasu bankuna da dama da wakilin namu ya leƙa, inda mutane ke shiga da fita suna karɓar tsaffin kuɗi.

Ita kuwa wata mata cewa ta yi tana fargabar karɓar tsofaffin takardun kuɗin amma kuma ta karɓa “ba don ranta na so ba”.

Ta ce ta karɓa ne saboda babu yadda za ta iya.

A kasuwar Tarauni, wani ɗan kasuwa ya ce tun da ya ji daga hukumomin Najeriya cewa a cigaba da karɓar tsaffin kuɗaɗen ba shi da wata damuwa.

A cewarsa, “Muna farin ciki da wannan abu da aka dawo a cigaba da karɓa saboda wahalar da mutane suke ciki na rashin sabon kuɗin sannan idan za a sayi abu a wajenmu, idan an yi ma transfer ba ya zuwa,

“Zan ci gaba da karɓa, kasuwanci zai cigaba yadda muke yi kamar da.” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here