Gwamnatin Saudiyya za ta ɗauki Mata 80 Direbobi a Filayen Jirgin Sama

 

Gwamnatin Saudiyya ta ce za ta ɗauki hayar mata sama da 80 a matsayin direbobi a manyan filayen jirgin sama na ƙasar guda huɗu.

Filayen jirgin sun haɗa da na Khalid da ke Riyadh da na Sarki Abdulaziz a Jeddah da na Sarki Fahd da ke birnin Dammam da kuma na Yarima Muhammad da ke Madinah.

Gwamnatin ƙasar ta ce hakan na cikin wani tsari da hukumar kula da sufuri ta ƙasar ta kaddamar a ranar Lahadi tare da haɗin gwiwar ma’aikatar albarkatun ƙasa da ci gaba, wanda aka yi domin sama wa mata aiki a bangaren sufuri, kamar yadda jaridar Al-Watan ta ruwait.

Ta ce tsarin ya haɗa da kirkiro da wani shiri da zai horar da matuka motocin da kuma bayar da taimakon agaji da sauransu. Hukumar ta ce tsarin zai kuma taimaka wajen ci gaban ɓangaren sufuri da yanda ake kula da fasinjoji don tabbatar da ɗorewar fannin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here