Magoya Bayan Jagoran ‘Yan Adawa na Pakistan, Imran Khan Sun yi Artabu da Ƴan Sanda

 

Magoya bayan jagoran ‘yan adawa na Pakistan Imrah Khan, sun yi artabu da ƴan sanda a wajen gidansa lokacin da suka yi yunkurin kama shi bayan da wata kotu ta bayar da umarnin yin haka.

Ƴan sandan sun harba hayaki mai sa kwalla don tarwasa dandazon mutane waɗanda suka yi jefa duwatsu kan jami’an.

A wani sakon bidiyo, Imran Khan ya bukaci magoya bayansa da su fito daga gidajensu domin ƙwatar yancinsu ko da an kai ga kama shi.

Hotuna da jam’iyyarsa ta watsa, sun nuna hayaki mai sa kwalla na faɗa wa kan gidan Imran Khan.

Tsohon Firaministan dai na fuskantar tuhuma kan sayar da wata kyauta da aka bai wa gwamnati lokacin da yake kan mulki.

Sai dai ya ce tuhumar na da alaƙa da siyasa.

naija gossip

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com