Daga Ado Abdullahi

Samun shugabanci nagari wajibi ne ga al’umma domin shi ne zai samar da rayuwa mai inganci da saita al’umma wajen samun kyakkyawan tsarin raya ƙasa na shekaru aru-aru masu zuwa.

Ɗaya daga cikin abin da ake son shugaba ya kasance yana da shi shi ne gaskiya da riƙon amana da sanin makamar aikin. Dole shugaban al’umma ya kasance mai ƙarfin zuciya wajen ɗaukar ƙaddarar rashin nasara kamar yadda ya kan sha yabo idan tsarinsa ya yi nasara daga jama’ar da yake mulka.

Riƙon sakainar kashi na dukiyar al’umma ko almubazzaranci da yin almundahana ko rub da ciki ko kashe-mu-raba na arziƙin ƙasa baya cikin tsarin shugabanci nagari.

Babu yadda al’umma za ta sami nutsuwa da zaman lafiya mai ɗorewa matuƙar basu da sahihin shugaba nagari.
Shugabanni nagari kamar yadda muke gani a wasu wurare idan sun yi wani kuskure wanda suke fuskantar wani zargi mai ƙwari, su kan ajiye muƙaminsu domin baiwa masu tuhumarsu damar bincike ba tare da yin katsalandan a aikinsu na bincike ba.

Duniyar shugabanci nagari ta yi gaba ta barmu a baya. Bamu da tsari irin na wayewa na ajiye muƙami a daidai lokacin da ake zargin shugaba da wani al’amari irin wannan. A daidai wannan gaɓa ina ganin wajibi ne mu jinjinawa tsohuwar ministan kuɗi wato Kemi Adesun, domin ajiye muƙami da ta yi kasancewar ana zarginta da badaƙalar yin amfani da takardar shaidar bautar ƙasa ta bogi. Lallai minista ta nuna ƙwarewa da jajircewa wajen nunawa shugabaninmu na Afirka abin da ya kamata su yi idan irin haka ta faru dasu.

Badaƙalar zargin karɓar na goro na zunzurutun kuɗi har naira Biliyan ɗaya da naira miliyan ɗari 800 daga hannun wasu ƴan kwangila lallai abin kunya ne da ya kamata mai girma gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi ta maza ya nuna dattaku ya ajiye muƙaminsa na gwamna, domin baiwa kwamitin da majalisar dokoki ta Kano ta kafa domin tabbatar da sahihancin waɗannan fayafayan bidiyo har 15 da aka gabatarwa majalisar, wanda wani fitaccen dan jarida a jihar ta Kano ya bijirarwa da kwamitin a kwanan baya.

Ga dukkanin alamu gwamnatin ta tsorata da yunƙurin wannan kwamiti na bincikar gaskiyar lamarin. Domin bayan ƙaryata zargin karɓar na goro da gwamnan ya yi a gaban kwamitin, ya kuma yi amfani da ƙarfinsa mulki wajen yin amfani da kotu don dakatar da binciken kwamitin. Akwai wani raɗeraɗin yunƙurin tsige shugaban majalisar ta jihar Kano a halin yanzu duk dai don hana ruwa gudu akan wannan bincike. Hausawa dai sun ce; idan ciki da gaskiya ai wuƙa ba ta huda shi. Shin dakatar da aikin kwamitin ba alamar gazawa bace daga ɓangaren gwamnati kuwa? Kuma wai shin ina barazanar gwamnatin Kano na maka ɗan jarida Jaafar Jaafar a kotu a bisa zargin ƙage ga gwamna Ganduje? Ko dai borin kunya ce kawai ?

Haka shirun gwamnatin tarayya da hukumominta na yaƙi da cin hanci da rashawa irin EFCC da ICPC ba ƙaramin naƙasu ba ce daga janibin gwamnatin tarayya, wacce take ta iƙirarin yaƙi da cin hanci da rashawa ba sani ba sabo.
Haka wannan ya saka shakku ga adalcin wannan gwamnati, domin dai an ga yadda hukumar EFCC ta yi uwa ta yi makarɓiya akan tuhumar gwamnan jihar Ekiti wato Kayode Fayose a lokacin yana gwamna. Inda hukumar ta kulle masa asusun banki kuma ta bayar da hujjah akan cewar tana da hurumin bincikar gwamnan mai ci a dukkanin wata badaƙala domin kare dukiyar al’umma.

To wai shin yaƙi da cin hancin da rashawar da ake yi bai shafi wani ɓangaren ƙasa bane sai waninsa ko kuwa bai shafi ɗan wata jam’iyya ba sai ɗan watanta?

Anya gwamnatin tarayya ba tufka da warwara take yi ba kuwa?

Lallai duniya ta zura ido ganin yadda za a gama wannan danbarwar. Shin majalisa za ta waske ta goyi bayan gwamna domin rufa masa asiri ko kuma rufawa juna asiri kamar yadda wasu mutane suke zargi? Ko kuwa zasu rufe ido su yi bincike na gaskiya domin ƙwato haƙƙin talakawan jihar Kano?

 

The post Badaƙalar Ganduje: Yaƙar Rashawa Ko Yaƙar Ƴan Adawa? appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here