Bayan EFCC ta Kama ta: An Bada Belin Matar Gwamna Ganduje, Hafsat Ganduje
An saki Hafsat Ganduje, matar gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje kan beli bayan hukumar yaki da rashawa da yi wa arzikin kasa ta’annati, EFCC, ta kama ta.
Daily Nigerian ta rawaito cewa an kama Hafsat Ganduje ne a yammacin ranar Litinin aka kuma tsare ta na tsawon awanni a hedkwatar hukumar EFCC da ke Abuja.
Ba a tabbatar ko a ofishin na EFCC ta kwana ba ko kuma ta sake komawa ne a safiyar ranar Talata, amma majiyoyi masu nagarta sun tabbatar cewa an ganta a ofishin EFCC a ranar Litinin da yamma da safiyar Talata.
Read Also:
Majiyoyi sun shaidawa Daily Nigerian cewa an bada belin ta a safiyar ranar Talata bayan ta cika ka’idojin belin da EFCC ta saka.
Jim kadan bayan bada belin, Hafsat Ganduje tare da mijinta gwamnan Kano da wasu iyalanta sun koma Kano a jirgin alfarma.
Dan Hafsat Ganduje na fari, Abdulazeez ne ya yi karar ta zuwa ofishin EFCC yana ikirarin cewa ta ta yi damfara a batun siyan fili da ya kai mata.
Dan nata ya yi korafin cewa wani mai gini ya bukaci ya taimaka masa ya siya wasu filaye a Kano inda ya bada daruruwan dalolin Amurka da kuma a kalla Naira Miliyan 35 a matsayin ‘kudin taimaka masa samun filin’.
Wani majiya da ke da masaniya kan lamarin ya ce:
“Amma bayan watanni uku, (mai ginin) ya gano cewa an sayar wa wani filayen da ya ke son siya don haka ya nemi a mayar masa da kudinsa.”