Bam ya Fashe a Babban Birnin Jihar Taraba
Mutane a birnin Jalingo na jihar Taraba sun shiga firgici, bayan wani abin fashewa ya fashe a birnin.
Abin fashewar wanda ake kyautata zaton bam ne ya fashe ne dai a wata matsaya da ke cikin birnin na Jalingo.
Ba a samu asarar rayuka ba, amma mutane da dama sun samun raunika, inda aka garzaya da su zuwa asibiti.
Jihar Taraba – Wani abin fashewa wanda ake kyautata zaton bam ne, ya fashe a daren ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Read Also:
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a wajen wata mashaya a Doruwa kusa da bankin Polaris, sannan ya shafi wasu gine-gine a yankin, yayin da mutane da dama waɗanda ba a san yawansu ba, suka samu raunika.
Channels Tv ta yi rahoto cewa wata budurwa ta samu mummunan rauni, inda aka garzaya da ita wani asibiti wanda ba a bayyana sunansa ba.
Ba a samu asarar rai ba a tashin bam ɗin, sai dai mutane da dama da suka samu raunika a dalilin fashewarsa.
Tuni jami’an ƴan sanda masu hana tashin bam suka zagaye wajen domin hana aukuwar tashin wani bam ɗin, idan har ta yiwu an dasa wani bam ɗin a kusa da wajen.
Tashin bam ɗin da ya auku a Doruwa, shine na huɗu da ya taɓa aukuwa a babban birnin jihar tun shekarar 2022, sannan na biyar da ya auku a jihar tun shekarar 2022.
Gwamnatin jihar Taraba da jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba, dangane da wannan lamarin har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.