Ƴan bindiga na Yin Hijira Daga Zamfara Zuwa Kaduna

 

Mazauna ƙauyukan Kaduna sun nuna damuwarsu tare da ankarar da cewa ‘yan bindiga da ke tsere wa luguden wutar da ake musu a Zamfara na samun mafaka a dazukan da ke kusa da su.

Garuruwan da ke iyaka tsakanin Zamfara da Kaduna ne suka fitar da wannan korafi, tare da cewa suna ganin ‘yan bindiga na yi musu shawagi.

Mazauna kauyen Damari a karamar hukumar Birnin Gwari sun ce ‘yan bindiga na shigar garuruwansu da tsakar rana.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya da ta wallafa labarin, ta kuma rawaito wani Saeed Damari da ke cewa tun ranar Talata ‘yan bindiga ke kwarara zuwa cikin dajin Kuduru.

Haka zalika shi ma wani mazaunin yankin ya shaida cewa ‘yan bindigar na yi musu barazanar garkuwa da manoma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here