Ban da Wata Matsala da Takarar da Atiku Yake yi – Wike

 

Nyesom Ezenwo Wike ya tabbatar da cewa bai da matsala da takarar da Atiku Abubakar yake yi.

Gwamnan jihar Ribas din yace yana goyon bayan Atiku/Okowa, amma sai an yi waje da Iyorchia Ayu.

Wike yana ganin ba adalci ba ne a hana ‘Yan Kudu komai, sai ‘Yan siyasan Arewa suyi baba-kere a PDP.

Rivers – Mai girma Gwamnan Ribas, Nyesom Ezenwo Wike yace bai da wani sabani da Atiku Abubakar mai takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP.

Daily Trust ta rahoto Mista Nyesom Ezenwo Wike yana cewa bai da matsala da ‘dan takaransu na 2023, illa iyaka dole a canza shugaban PDP na Najeriya.

Wike ya fadawa manyan PDP wannan ne bayan jam’iyyar ta tsaida yakin neman zaben shugaban kasa cak, saboda ta shawo kan shi da ‘yan bangarensa.

Jaridar ta rahoto Gwamnan ya na bayani a lokacin da ya zauna da ‘yan takaran jam’yyar PDP na gwamna da sauran kujerun majalisa a jihar Kuros Riba.

Inda aka samu matsala a wajen sulhu A nan ne Wike ya shaidawa ‘yan takaran cewa wasu ‘yan bani-na-iya suka hana a sasanta tsakanin mutanensa da ake rikici da su a jam’iyyar adawar.

Tsohon Ministan yace babu wanda zai iya canza masa ra’ayin da yake da shi na cewa ya kamata kujerar shugaban jam’iyya ta dawo kudancin kasar nan.

Mataimakin shugaban PDP na shiyyar Kudu maso kudu, Dan Orbih yana cikin wadanda suke halarce a lokacin da Gwamnan na Ribas yake magana.

Mun gama zaben ‘dan takaran shugaban kasa, muna da ‘dan takara. Shin Wike yana cewa a cire ‘dan takarar shugaban kasa ne?

Shin Wike yana cewa a cire ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa ne?

A kan me ake bani hakuri? Abin da nake cewa kuma zan cigaba da fada shi ne, kun dauki shugaban kasa, sai ku ba mu kujerar shugaban jam’iyya na kasa!

– Nyesom Wike

Ba ayi wa Kudu adalci a PDP ba

A ra’ayin ‘dan siyasar, babu adalci idan ‘Yan Arewa suka rike ‘dan takara, shugaban jam’iyya da kuma Darekta Janar na kwamitin zaben shugaban kasa.

“Na karbi ‘dan takarar shugaban kasar, na karbi ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar.

Mene kuma? Ya rage naku, ku ba ‘Yan Kudu wani abu, shikenan.” – Nyesom Wike

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here