Kotu ta Sallami Shugaba Kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu

 

FCT Abuja – Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sallami shugaban haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, Channels Television ta rahoto.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gurfanar da Kanu ne a babban kotun tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume 15 masu alaka da cin amanar kasa da ta’addanci da ta ke zargin ya aikata yayin fafutikan neman ballewa daga Najeriya.

Alkalai uku a kotun daukaka kara sun ce babban kotun na tarayya ba ta da hurumin yi masa shari’a duba da cewa yadda aka sace shi aka dawo da shi Najeriya ya saba wa dokokin OAU.

Kotun ta ce tuhume-tuhume 15 da aka yi wa Kanu bai bayyana wuri, rana, lokaci da yanayin laifukan da ya aikata ba kafin a dawo da shi Najeriya ba bisa ka’ida ba, tare da saba dokokin kasa da kasa.

Kotun ta kara da cewa gwamnatin tarayya ta gaza bayyana inda aka kama Nnamdi Kanu duk da irin manyan zargin da ta ke masa.

Dakaci karin bayani …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here