Bayan Rigakafin Korona: ‘Dan Majalisar Wakilan Amurka ya Kamu da Cutar
Dan majalisar wakilan Amurka, Kevin Brady, ya bayyanawa duniya ranar Laraba cewa ya kamu da cutar Korona bayan karban rigakafin Pfizer-BioNTech na farko.
A ka’ida sau biyu mutum zai karbi alluran rigakafin makonni uku tsakani.
Read Also:
“Da daren nan, Likitan majalisa ya sanar da ni cewa na kamu da cutar COVID-19 kuma ina killace,” ya bayyana a Tuwita.
“Kamar da yadda aka bada shawara, na karbi rigakafin Pfizer ranar 18 ga Disamba kuma ko a ranar sabuwar shekara na yi gwaji amma ban da cutar.”
Yanzu haka an amince da amfani da rigakafin cutar Korona iri biyu a kasar Amurka. Na kamfanin Pfizer wanda ake karba sau biyu makonni uku tsakani, da kuma kamfanin Moderna, wanda ake karba sau biyu wata daya tsakani.