An Cigaba da Shirya Fim Din Gidan Badamasi Zango na Uku

Nasashshen nishadi mai cike da nason kayatarwa na kwankwasa kofar ma’abota abotar kallon kayataccen shirin nan na ” Gidan Badamasi” wanda ahalin yanzu anfara daukar zango na uku.

Shirin da yasamu zaren zarafin filin fitowar manyan Jarumai irin su: Jaruma Hadiza Gabon, Magaji Mijinyawa, Mustapha Naburuska, Nura Dandolo, Ado Isah Gwanja, Tijjani Asase, Hauwa Ayawa, dasauransu.

Gidan Badamasi shiri ne wanda aka gina zaren labarinsa akan wani magidanci mai matukar arziki, wanda a gefe guda ya toshe dukkan wata kafa da kofa dazata sadar da kokon igiyar da ‘ya yansa ke rarrafowa da ita domin zargo arzikin ta kowace hanya,hakan nasu ya gaza cimma ruwa,dalilian dayasa suke ta fatan ” Allah yakar giwa mu ci nama”.

Kamar yadda ake wa shirin lakabi da ” Maganin hawan jini kyauta” .

shiri ne wanda gidan talabijin na Arewa24 ke haskawa, Kamfanin Dorayi Film and Distribution Limited suka dauki nauyi tare da hadin gwiwar Nazir Adam Salihi, Falalu A.

Dorayi ya bada umarni.

” Zango na farko da zango na biyun shirin sun zama gagarumar nasara, domin sun nishadantar matuka gaya, sun kuma ilimantar damu haikan hakikatan mu masu kallo cikin wani salo na kwarewa.

” Inji Musa Khan, wani daga cikin ma’abota kallon Fina finai kuma mai jiran fitowar shirin Gidan Badamasi zango na uku.

Darakta Falalu A. Dorayi ya bayyana cewar a shirya ganin kaifaffan nishadi a wannan zango na ukun.

Bila shakkin masu kallo su gyara zaman ganin wasu sirrin masarurin sinadaran nishadi da darasi a saisaice a cikin shirin Gidan Badamasi zango na uku.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here