Gwamnatin Tarayya Bazata Samu Damar Biyan Wasu hukumomi Albashin Watan Nuwamba
Akalla hukumomi 428 ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba.
Ben Akabueze, shugaban ofishin kasafi, ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisa.
A cewar Akabueze, karin albashin da aka yi ne bayan kammala kasafin shekarar 2019 ne dalilin faruwar hakan Gwammatin tarayya ta ce aƙalla hukumomi 428 ne wanda ba zasu iya biyan albashin ma’aikatansu ba a ƙarshen watan Nuwamba 2020.
Shugaban ofishin kasafin kuɗi, Ben Akabueze,ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da gurfana gaban kwamitin Sanatoci akan asusun al’umma wato baitul mali.
Read Also:
Yace dalilin hakan shine an riga an gama tsara kasafin kuɗin shekarar 2019 kafin gwamnatin tarayya ta sanar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.
Akabueze yace tuni gwamnatin tarayya ta fara shiryen sakin kuɗaɗe daga Asusun ko ta kwana na SWV (Service Wide Vote) don cike giɓin da aka samu domin biyan albashin watan Nuwamba, a cewarsa.
Kazalika, shugaban kwamitin, Sanata Mathew Urhoghide, ya zargi ɓangaren zartarwa da rage adadin kuɗaɗen ofishin babban Oditan tarayya da gayya.
Ya bayyana mamakinsa a fili, ganin yadda aka ragewa hukumar da aka ƙirƙira don yaƙar rashawa kuɗaɗen gudanarwa daga ɓangaren zartawa, inda kuma sauran hukumomi kamar ICPC da EFCC aka ware musu kuɗin da ya kamata.
Da yake maida bayani, Akabueze ya ce ofishin kasafin kuɗi zai tura kuɗaɗe ne ofishin babban Odita bisa tsarin da doka ta tanada idan akwai buƙatar hakan.