Wanda suka Bar Boko Haram su Suka Kashe Kanal D.C Bako – Ali Ndume

Tubabbun ‘yan Boko Haram ne suka yi sanadiyyar mutuwar Kanal D.C. Bako, cewar Sanatan jihar Borno, Ali Ndume.

Ndume ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, inda ya ce sam ba za ta sabu ba, bindiga a ruwa – Ya ce tubabbun ‘yan Boko Haram su na cigaba da ta’addanci, don haka wajibi ne gwamnati ta daina tallafa musu tana fifita su Tubabbun ‘yan Boko Haram ne sukayi sanadin mutuwar kanal din sojojin kasa, Premium Times ta wallafa.

Tubabben dan Boko Haram ne yayi sanadin kisan wani Kanal na sojojin kasa, Kanal D.C Bako, a cewar sanatan jihar Borno, Ali Ndume.

A cewarsa, tubabben dan Boko Haram din ne ya bayar da bayanai a kan Kanal din.

An kashe Bako a ranar 21 ga watan Satumba a wani karon batta da suka yi da ‘yan Boko Haram din, kusa da Damboa, wani gari da bai wuce kilomita 85 da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Bayan tabbatar da mutuwarsa, rundunar sojin kasa sun kwatanta D.C Bako a matsayin gwarzo kuma jarumin soja.

Ndume, wanda shine shugaban kwamitin sojojin kasa na majalisar dattawa, ya sanar da manema labarai hakan a ranar Laraba, bayan bayyana kasafin rundunar soji.

Sanatan ya amsa tambayar da aka yi masa a kan samar da kudade ga sojoji da kuma taimakon tubabbun ‘yan Boko Haram da suka koma anguwanninsu.

Ya ce “Gaskiya ban amince da yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram ba.

Ba za a cigaba da fifita su ba a kan mutane.

Na tabbatar da cewa mafi yawan ‘yan Najeriya ba za su goyi bayan cigaba da tallafa musu ba.

“A kauyenmu, an saci malamai da manya akalla masu shekaru 60, kusan su 75.

‘Yan Boko Haram suka kai su mayanka suka kashesu.

Ta yaya za a yi a ce har yanzu Najeriya tana taimakon tubabbun ‘yan Boko Haram?”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here