ALLAH ya yi wa Kwamishinan lafiya – Emmanuel Ikwulonu Rasuwa

Allah ya yiwa kwamishinan lafiya na jihar Benue, Dr Emmanuel Ikwulonu, rasuwa.

An tattaro cewa an yi wa Ikwulonu tiyata na wani rashin lafiya da ba a bayyana ba, amma sai abun ya zo da matsala wanda ya kai ga mutuwarsa Wata majiya ta gidan gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar nasa Kwamishinan lafiya na jihar Benue, Dr Emmanuel Ikwulonu, ya rasu, Nigerian Tribune ta ruwaito.

A ranar 5 ga watan Agustan 2020 ne aka rantsar da Dr Ikwulonu a matsayin kwamishinan lafiya da harkokin jama’a na jihar Benue.

Ya maye gurbin Dr Sunday Ongbabo wanda ya yi murabus daga majalisar zartarwa ta jihar.

Wata majiya ta gidan gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa kwamishinan wanda aka ba gado a asibiti ya mutu sakamakon rashin nasara da aka samu a aikin tiyata da aka yi masa na wani ciwo da ba a bayyana ba.

“Ya halarci zaman majalisar zartarwar jihar da aka gudn benuear na karshe a makon da ya gabata sannan ya je aka yi masa aiki.

“Mutuwarsa ya zo kamar almara a yammacin nan,” in ji majiyar gwamnatin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here