Rijiyar Barhout: Masana Kimiyya Sun Fara Bincike a Kogon Kare Kukanka Dake Yemen
Tawagar masana kimiyya daga Oman sun fara binciken wani babban kogo a Yemen da aka fi sani da Rijiyar Barhout a karon farko.
Babban ramin yana cikin hamadar al-Mahra.
Read Also:
An dade ana alakanta wajen da abubuwan ban tsoro, har ta kai ga ana yi masa kirari da kogon kare kukanka.
Wasu labaran ma da aka rika bayarwa na cewa nan ne aka daure tarin aljanun duniya da dama.
Hotunan da masana kimiyyar suka fara aikowa sun nuna tarin macizai, da kwaɗi da da ƙudan zuma cunkus a makeken kogon, baya ga wasu irin halittu da tsayinsu ya zarce mita 9.