Karbo 4.9bn: Jahohin da Zasu fi Amfana da Bashin

 

Gwamnatin Tarayya tana neman a bata dama ta karbo $4.9bn daga kasar waje.

Jahohin Kano, Legas Taraba, Nasarawa, da Kogi za su amfana idan aka ci bashin.

Za a narka wani kaso daga cikin kudin a aikin jirgin kasan Maradi da na Ibadan.

Abuja – Titin dogon jirgin kasan Kano zuwa garin Maradi a kasar Nijar yana cikin ayyukan da ake sa rai za ayi da sabon bashin da gwamnati take nema.

Jaridar Punch ta rahoto shugaban kasa yana so majalisa ta amince masa ya karbo bashi domin a aiwatar da wasu ayyuka a cikin tsare-tsaren 2018-2020.

A wasikar da shugaban kasa ya aika wa ‘yan majalisa a baya, ya bayyana cewa za a yi wa kowane yankin kasar nan ayyuka da makudan kudin da za a aro.

Dogon Kano-Katsina-Daura-Jibiya-Maradi

Majiyar jaridar ta bayyana cewa da wannan tulin bashi ne za a soma aikin titin jirgin kasan Kano-Maradi, wanda za a tsaya a garin Dutse, jahar Jigawa.

Shugaba Muhammadu Buhari yace jirgin kasan da zai hada Kano-Katsina-Daura-Jibiya-Maradi zai bunkasa kasuwancin Najeriya da Arewacin Afrika.

Legas za ta ci moriyar bashin

Idan an karbo aron kudin ne za ayi amfani da fam $225,120,000 daga bankin China Exim Bank domin a kammala titin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan.

A yankin Kudu maso yamma, za ayi aiki a tashoshin ruwan Apapa da Tincan da wannan bashin.

Sauran jahohin da za su ci moriyar bashin kudin sun hada da; Anambra, Benuwai, Ebonyi, Neja, Ogun. Sai kuma jahohin Taraba, Nasarawa, Enugu da jahar Kogi.

Ana sa rai kudin da za a karbo ya kai ga manoma 100, 000 da masu gyaran kayan hatsi 3, 000. Har ila yau ‘yan kasuwa 6, 000 aka yi kasafi za su amfana da bashin.

Rahoton yace Bankin Sin zai taimaka da $276,981,587 daga cikin kudin, wanda za ayi amfani da shi wajen bunkasa harkar wutar lantarki a wasu wurare a kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here