Dalilin da Yasa ba za mu Binciki Masu Siyan Fom Din Takara na N100m ba – Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa ta magantu a kan dalilin da yasa Shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya bincikar masu siyan fom din takara na naira miliyan 100 ba.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce hakkin kungiyoyin jama’a da hukumar yaki da rashawa ne su gano tushen kudaden masu takarar.

Ya kuma bayyana cewa umarnin shugaban kasar na cewa ministoci da sauran masu neman mukamai su yi murabus daga mukamansu bai shafi sashe na 84 na dokar zabe ba.

Abuja – Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaban kasar ba zai binciki yadda yan takara suka samu kudaden da suka kashe wajen siyan fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin Channels TV a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Akalla yan takara fiye da 30 ne suka yanki tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, amma Shehu ya bayyana cewa aikin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da kungiyoyin jama’a ne gano yadda aka yi suka samu wannan kudi ba wai aikin shugaban kasa ba.

Ya ce:

“Tambayar shine ya aka yi suka samu naira miliyan 100 suka siya fom? Ina ganin ya kamata tambayar ta je ga kowani dan takara ne. Irin wannan bincike ya rataya ne a wuya kungiyoyin jama’a sannan kafafen yada labarai su rika yin tambayoyi, amma suna cewa shugaban kasa ya yi bincike, ba na tunanin wannan ne mafita.

“Idan ICPC ko EFCC za su ce ‘Ya sakataren dindindin, daga ina ka samu wannan kudin?, shugaban kasar ba zai hana su ba.”

Yakamata a yabawa fom din na naira miliyan 100

A cewar Shehu, yakamata a yabama farashin fom din shugaban kasar na APC domin jam’iyyar na bukatar kudin gudanar da harkokin zabenta.

Ya ce:

“Jam’iyyar ta yi bayani kan wannan batu kuma an yaba wa shugaban jam’iyyar na kasa saboda wannan jam’iyya ce da ba ta karbar kudi daga baitulmalin kasar.”

A halin da ake ciki, Shehu ya ce umarnin shugaban kasar na cewa ministoci, shugabannin hukumomi da sauran masu neman mukamai su yi murabus daga mukamansu bai shafi sashe na 84 na dokar zabe ba, Sahara Reporters ta rahoto.

“Bai yi magana kan sashe na 84 ba, kawai ya ba da umarnin kuma ina ganin a fili yake cewa a matsayinsa na shugaban bangaren zartarwa na gwamnati, shi ne ke da ikon zartarwa da yanke hukunci.”

Ya kawar da fargabar cewa za a samu baraka a gwamnati biyo bayan umarnin shugaban kasar.

Ya ci gaba da cewa:

“Shugaban ya ba da umarninsa, ya fayyace komai ya rage ga kowa ya kama inda zai je.

“Umurnin da gwamnati ta bayar shine cewa idan kai minista ne kuma kana da karamin minista, ka mika masa mulki. Idan baka da karamin minista, ka mikawa sakataren dindindin.

Idan kai shugaban hukumar gwamnati ne, jakada, ka mika mulki ga babban jami’i a sashin ka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here