FG: Buhari na Ganawa da Shugabannin Tsaro
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na yin wata ganawa da shugabannin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa ta Villa, a cewar Bashir Ahmad mai taimaka wa shugaban kan kafafen sada zumunta.
Read Also:
Daga cikin waɗanda ke halartar taron akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnati da Ministan Tsaro da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da shugabannin sojoji.
Fadar gwamnatin Najeriya na cigaba da gudanar da taruka ne domin lalubo hanyoyin biyan buƙatar masu zanga-zangar EndSars, wadda ta rikiɗe zuwa tashin hankali a wasu sassan ƙasar.
Jihohi da dama sun saka dokar hana fita sakamakon rikicin, inda a Legas aka ƙona gidan jaridun The Nation da TVC tare da yashe wasu manyan kantunan kasuwanci.