Shugaba Buhari ya Kaddamar da Cibiyar Yada Al’adun Yarbawa a Legas

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata cibiya ta yada al’adun Yarbawa a jihar Legas.

Buhari ya kai ziyara jihar ta Legas ne domin kaddamar da ayyukan da gwamna Sanwo-Olu ya yi a jihar.

Shugaban na ci gaba da yawo a jihohin kasar nan don yin kamfen na APC da kuma kaddamar da ayyuka.

Jihar Legas – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da cibiyar John Randle ta kiyayewa da yada al’adu da tarihin Yarbawa a jihar Legas.

Shugaban ya kaddamar da aikin ne a ranar Talata 24 ga watan Janairu yayin wata ziyara a jihar, jaridar Punch ta ruwaito.

A lokacin kaddamarwar, Buhari yana tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwushi da dai sauran jiga-jigan yankin.

Idan baku manta ba shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Legas domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin APC ta Sanwo-Olu ta yiwa jihar.

Ya kasance a jihar Legas tun ranar Litinin 23 ga watan Janairu jim kadan bayan kammala gangamin kamfen na APC a jihar Bauchi.

Martanin jama’a a Twitter

Bayan da jaridar ta yada bidiyon shugaban a jihar Legas lokacin da yake kaddamar da aikin, mutane da yawa sun yi matani. Ga kadan daga ciki:

“Allah ya yi albarka Baba Buhari.”

@Letsgonow10

“Wannan abu namu ne (Yarbawa), amma abin haushi Bafulatani ne mai bude shi.”

@_Konrade

“Yarbawa sun kare gobensu, kuma za su iya yin alfahari da hakan. Shugabanninsu, duk da bambancinsu, kansu a hade yake.”

@teewesthojo

“Shin cewa kuka yi tarihi ko salsala?”

 

 

latest naija news

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here